Kalifa Malam Muhammadu Sanusi II A Mahangar Marubuta  

Sanusi

Daga Mahmud Indabawa,

Mukamin Khalifancin Darikar Tijjaniya a Nijeriya tarihi ne ya maimata kansa, domin marubuta tuni su kayi gudu harda zamiya ta fuskar fito da abubuwan mamakin  Khalifa Muhammad Sanusi II, domin ba alfarma ba ce yi masa Khalifancin Tijjaniyya a Nijeriya, domin Kakansu Muhammadu Sausi I ya zama Khalifan Tijjaniyya kafin komawarsa ga Allah, haka kuma Muhammadu Sanusi I ya zama Sarkin Kano, an sauke kakansa daga sarautar Kano inda aka mayar da shi garin Azare kafin daga baya Marigayi Abubakar Rimi  ya maido shi Garin Wudil, shi ma Muhammadu Sausi II ya zama Sarkin Kano, sannan an sauke shi daga sarautar Kano inda aka maida shi Jihar Nasarawa kafin daga baya a mayar da shi Jihar Legas

 

Watakila mai karatu ya yi tuna ni ko tambayar cewa ko me wannan marubucin yake nufi da mukami ko matsayi karo na uku baicin kakannasa, a saninmu Sarkin Kano ya yi bayan ya yi murabus aka nada shi Halifan Darikar Tijjaniyya haka shi ma Sanusi na biyu, Sarkin Kano ya yi bayan saukarsa yanzu aka nada shi Halifan Tijjaniyya.

 

To a ina Sanusi na biyu ya gaji kakansa karo na uku, mai karatu idan ka yi wannan tunani ko tambaya ni ba zan ga laifinka ba, dalili Magana ce ta ilimi da tarihi, musamman shi tarihi har kullum idan ka ga ya dawo to sake maimaita kansa yake yi don ba a wannan ya faru ba, ko dai ya zo da sunansa da kamanninsa na ainihi ko ya canja, amma dai su ne abubuwa guda biyu ko uku watakila za su sa ba za ka gano haka ba, ko dai ba ka da cikakkiyar masaniyar tushen abin, na biyu ko ba ka da alkaluman lissafin abin a hannunka, na uku ko ba ka da ilimi mai zurfi a kan wannan bangaren da zai hanaka gano hakan. Shi kansa Mai Martaba Sanusi na biyu duk abin da ya aikata ko ya yi nuni da shi tarihi ne ya sa yake maimaita kansa da shi.

Mai karatu ka yi hakuri ka biyo a hankali ni da kai watakila ko ma gano bakin zaren a inda shi Malam Sanusi na biyu ya gaji kakansa dai-dai har karo uku. Amma ba za mu fahimci hakan ba har sai mun koma ga tarihi, misali a lokacin da Shehu Usman Danfodio (Allah ya kara jaddada rahama a gareshi) yake gwagwarmayar jaddada addinin Musulunci in da ya yi fama da Sarkin Gobir Bawa Jan Gwarzo shi da ‘ya`yansa Yumfa na Fata da dai sauransu.  Bayan nasarar Shehu Usman Danfodio an dawo da addinin Musulunci ainihin koyarwar Manzon Allah (SAW) sai bayar da tuta ga manyan garuruwa irinsu Katsina, Kano, Zaria, Gombe, Adamawa, Ilorin, Bauchi da dai sauransu ma’ana yana da malamai masu ilimi da jagorantarwa a can garuruwa, wato bayan kawar da mulkin sarakunan “Habe” sai suka zama su ne sarakai su ne Malamai su ne alkalai saboda haka har zuwa lokacin da turawan mulkin mallaka suka kawar da Daular mulkin Shehu Usman Danfodio a wadannan kasashe duk wanda za a nada shi Malami ne mai ilimi kan maganar gado, amma da turawa suke zo sai jagorancin ya koma jini ake bi wato gado, da ya gaji babansa ko kakansa ko wan babansa ko kani.

 

Amma turawa sun zo da nasu tsare-tsaren shugabanci suke kara nasu, kuma suka soke wadansu kamar yanke hannun barawo, jefe mazinata da dai sauransu, daga cikin wadanda turawa suka barwa sarakuna su aiwatar har da kananan shari’o’i kamar rabon gado, rigingimun aure da sauransu.

 

Wanda Shehu Usman Danfodio ya bai wa tuta a nan kasar Kano shi ne Malam Sulaiman, an tabbatar da cewa tun daga kan Sarki Sulaiman har zuwa kan Sarki Malam Sanusi na daya idan ana lissafi Sarakunan Kano masu dimbin ilimi to Malam Sanusi na daya ba zai ketare na uku ba ko dai na biyu ba, shi ne Sarki shi ne alkali shi ne Malami, da safe idan an gama gaisuwa a fada sai ya ya matsa kadan ya hau kan karagar Alkali, yamma tana yi sai ya hau kan shimfidar buzun karatu.

 

Gado na farko na kakansa da Malam Sanusi na biyu ya fara yi shi ne ilimi, duk  da cewa cikin abu guda uku ana iya gadar guda biyu ko ayi karya dasu, amma banda guda daya shi ne ilimi, idan babanka ko kakanka Sarki ne kana iya gadonsa, haka idan babanka attajiri ne kana iya gadonsa, hakama idan babanka ko kakanka jarumi ne ko wani shakiyi marar mutunci kana iya gadonsa, domin ance sau da yawa ‘ya’ya ko jikoki su kan gaji iyayen su ko kakanninsu ta wajen ilimi, halaye ko dabi’u da sauransu.

Haka ma kana iya nadi wata kila harka fitar da kunnuwa guda biyu kamar yadda ‘ya’yan Sarakai su keyi, ga alkyabba, haka ma kana iya ciko jakarka da kudi ka tara maroka da makada kayi ta bushasharka kana cewa kai dan attajiri wane ne ko jikan maikudi wane ne.

 

Amman ilimi ba’a gadarsa ko karyarsa dole sai kayi shi, misali don kakanka ko babanka wani babban Shehin Malami ne yana da wansa ko kane ba za’a wayi gari kawai ka zama mai ilimi ba.

 

Haka ma ba zaka yi karyar cewa kai mai ilimi ne ba, furta kalma daya zuwa uku za’a san karya ka keyi, don shi mai ilimi ko da hira akeyi dashi ta duniya ba sai ya ja ma aya ko hadisi ba yana fara magana za’a fahimci mai ilimi ne shi.

Bayan Malam Muhammadu Sanusi na biyu ya koshi kuma ya tumbatsa da ilimin zamani watau boko sai ya dukkufa neman ilimin addini,  bai tsaya iyakar sanin gane hukunce hukunce gyaran sallah alwala da dai sauransu ba, said a tumbatsa a ilimi mai zurfi na sanin hukunce hukuncen masu sarkakkiya.

 

Mai karatu watakila ka yarda dani idan nace ma wadannan misalai dana bayar kadan ne daga cikin dalilan dana dogara dasu har nace Mai Martaba Muhammadu Sanusi na biyu ya gaji kakansa har karo uku, duk da cewa kamar yadda na fada a baya ilimi ba’a gadonsa sai kayi da gabobinka kamar baki, hannu kafa idanu da dai sauransu.

 

A lokacin da Mai Martaba Sanusi na biyu yake Sarkin Kano, w dokar nan ta shekarar “1976” wacce ta karbe ikon nada Alkali, da ‘yan doka da jami’an gidan kurkuku, da ikon harkar kasa da safiyo da dai sauransu, wacce mai alfamar Sarkin Musulmi Dasuki, in har dokar ta samu sunan lakanin Ibrahim Dasuki (Rufom) da Mai Martaba Sanusi na biyu bayan gama zama, komawa zaiyi ha harde akan karagar Alkali ya ci gaba da yin alkalanci ta dukkan abinda ya shafi shari’a kowacce iri ce. Domin mu talakawan Kano shaida ne lokacin da yake Sarkin Kano shi yake yin limancin sallar juma’a da limancin sallar idi karama da babbar sallah, kuma wani abin sha’awa da burgewa duk hudubar da zaiyi ta juma’ace ko ta idi abinda yake faruwa alokacin akansa zai yi huduba, misali tauye mudu ga ‘yan kasuwa, zamba cikin aminci, rashin adalci ga shugabannin al’umma sakacin iyaye akan ‘ya’yansu, rashin adalcin mazaje akan matansu da dai makamantansu.

 

Alokacin da Mai Martaba Malam Sanusi na biyu yake rike da kujerar Gwamnan Babban Bankin Nijeriya ni kuma alokacin wasu dalilai sun sani kasa zama a Nijeriya na tafi zuwa kasar Misra, watau Masar, amma mai karatu kayi hakuri bazan gaya ma ga irin abinda ya fitar da ni daga Nijeriya ba wannan ni kadai ya shafa da iyalina.

 

Bayan saukata a babban filin jirgin saman kasar watau “Kairo” mu’amalar farko dana farayi da bankunan da suke cikin filin jirgin saman da kuma irin manyan kantuna dakanana da suke aciki tun a nan na fara ganin canji na tattalin arziki da suka sha babban da kasa ta, haka ma zaman da nayi akasar da dukkan wata mu’amala da wasu ‘yan huddodi nayi yasa na fahimci akwai tazara mai yawa a tsakaninmu dasu, saboda haka sai kishi da son cigaban kasa ta ya kamani ko ya murdamin a zuciyata.

 

Duk da cewa ni ba masanin tattalin arzikin bane, amma nayi karambanin kaiwa mai Girma Gwamnan Babban Bankin Nijeriya shawara wanda ina ganin idan aka aiwatar da ita kasa ta zata amfana da irin tsarin kuma kai tsaye kujerar Gwamnan Babban Banki kasata ya fi nasu shahara, nayi dogon bayani na dukkanin irin abinda na gani da wanda naji da kunnena.

 

Bayan abin da ya shafi tattalin arzikin kasa sai nake cewa ina ji ajikina nan gaba akwai yiwuwar Malam Muhammadu Sanusi zai gaji rawanin kakansa Sarkin Kano mai murabus Malam Muhammadu Sanusi na daya. Na kuma kwana da sanin cewa ni ba masanin ilimin taurari bane, amman matsayina na ba Kano kuma Marubuci mai nazari da sharhi da fashin baki, kuma mai bibiyar al’amuran yau da kullum wannan hasashe nawa mai yiwuwa ne, sai na kara da cewa idan Allah ya karbi addu’armu talakawan Kano Mai Girma Malam Sanusi ya gaji rawanin kakansa tabbas za’a kawo chanje chanje da zamanantar da masarautar Kano.

 

Jaridar LEADERSHIP HAUSA ta ranar Juma’a (25/3/2011) ta buga wannan karambanin nawa hakama Jaridar Albishir  mallakar Gwamnatin Kano ta ranar Laraba (7/12/2011) itama ta buga kuma na baiwa rubutun nawa suna TAFIYA MABUDIN ILIMI TSARABA GA ‘YAN NIJERIYA DAGA MASAR.

 

Bayan na dawo Najeriya sai Allah ya karbi addu’armu Mai Girma Gwamnan Babban Banki Najeriya ya zama Sarkin Kano watau ya gaji rawanin Kakansa, bayan zama Sarkin Kano, tabbas hasashen da nayi sai da ya zama gaskiya, domin ya zamanantar da Masarautar Kano hakama ya kawo chanje chanje masu yawa a Masarautar Kano, hatta tsarin tsofaffin gine ginen cikin fadar Masarautar wadanda suka yi shekaru ya chanjasu da zamanantar dasu.

 

Dama shi Mai Martaba Halifa Sanusi na biyu tarihin rayuwarsa tun yana dan makaranta zuwa aikace aikacen da yayi har zuwa Sarkin Kano kafin ya bar gurin sai yakafa tarihi a wurin, ma’ana zai kawo chanje chanje da zamanantar wurin. Ba karshen wannan tsokacina bayan taya murna da fatan alkhairi ga Mai Martaba Halifa zan sake yin wani shishigi da karambani da shawara ga shi kansa Halifa, bayan hada kan Yan Darikar Tijjaniyya su zama tsintsiya madaurinki daya, kana Najeriya ka dai ba har na dukkan baki daya, Halifa zai bude wani shafi ko dandali ayanar gizogizo duk wanda yake neman bayani akan darikar keta ba tare da bata lokaci ba zai gani. Kamar yadda nake gani was kungiyoyin addini bayan jaridu har gidajen radio da talabijin suke dasu na san Mai Martaba Halifa zai yi amfani alokacin shugabancinsa ga Darikar zaiyi haka.

 

Ranka ya dade Allah ya taimaki Halifa lokaci zuwa lokaci akan sami sakin baki fiyayyen Halitta Manzon Allah (SAW) ga yan Darikar musamman anfi samun hakan a wajen “Sha’irai” watau masu yabo saboda shauki da son Manzon Allah (SAW) sai kaji an yansokeke agareshi wanda ya na kawo cecekuce da ta jijiyar wuya atsakanin wadanda mabiya darikar bane, kai har ma a cikin magoya bayan darikar.

 

Ni shawarata anan ga Mai Martaba Halifa itace akafa wani karfaffen kwamiti a kowacce “Zawuya” aikinsa shine duk wani sha’iri kafin ya saki kasidarsa sai ya kawo gaban wannan kwamiti sun tace sannan su bashi izinin rerewa.

 

Mai Martaba Halifa wadansu mutane dake gefe musamman masu adawa da darikun sufaye suna kallo ko fassara darikar Tijjaniyya dace watabigitajiyar darikace tsawon shekaru daruruwa da kafata amma taki karbar canje canjen zamani ta bar magoyabayanta duk da cewa har yanzu yanke shawarar karbar darikarba amman kusancina na kud da kud da wasu daga cikin manyan darikar misali kakana tun ina yaro nake ganin ana zuwa wajensa karbar darikar Tijjaniyya haka ma Malamine wanda nake daukar karatu awajensa, hakama duk wata fatawa da dauremin kai wajensa zanje ya warwaremin ita.

Malamin nawa shi ne Al-Sheikh Ahmad Tijjani Mai Salati Indabawa shugaban Kungiyar “Fityanatul Islam” ta nan Jahar Kano, kuma babban Darakta a ma’aikatar ilimi ta Jahar Kano. Wadannan dalilai guda biyu sun bani dama ne san wani abu kadan acikin Darikar.

 

Kamar yadda nace a baya a matsayina na marubuci mai sharhi da bibiyar al’amuran yau da kullum hakika ina da yar gudummawar da zan iya bayarwa ga darikar ko da ta shawara ce ta fefen baki kuwa.

 

Daga karshe ina fata da rokon Allah ya taimaki Mai Martaba Halifa Sanusi na biyu Allah yayi riko da hannunka yayima jagora wajen sauke wannan nauyin da aka doramaka amin summa amin.

 

Mahmud Abdullahi Indabawa

08055101909, 08132013037

E-mail: mahmudabdullahi@gmail.com 

 

Exit mobile version