Tare da Rukayya Ayyuba Adamu
Hakkin da ya ke rataye a wuyanki a matsayinkina uwa ga danta, ba wai kawai ki tabbatar da ya ci abinci ba ne kurum. A garekilallai akwai wani gagarumin aiki. Aikin nan kuwa shi ne na ganin kin yi kokarin zama uwa mai daura damarar cusawa danta tsarin gudanar da rayuwa mai inganci. Wanda hakan zai bayar da gudunmuwa mai tarin yawa game da kawo gyara ga dabi’un al’ummarmu a yau, watakila gyaran da za ki yi a matsayinki na uwa ya rage wa al’umma fargaba wanda rashin aminci ke kawowa a tsakanin mutane. Ga kuma rigingimu da ake ta fama da suwadanda ke da alaka kai tsaye da tabarbarewar tarbiyya da muke ta fama da su a yau.
Da farko dai alhakinki ne kidasa wa danki kyawawan halaye ta hanyar sa shi ya zama mai tsoron mahaliccinsa kurum. Sannan kuma kirabashi da wani tsoronna abinda aka halitta, domin ya zama jarumi.Tabbas ubangijin da ya halicci dan nan na ki, kuma ya kaddara ki a matsayin uwarshi sai ya tambayeki game da yadda kika rike amanar kulawa da shi.
Hakika kula da tarbiyyar yara ya isheki babban aiki. Idan ki ka tsaya tsayin daka a kan bayar da ita yadda ya kamata, to hakika kin bayar da gagarumar gudummuwa wajen samar da al’umma lafiyayyiya, kuma nagartacciya.Akwai isharori da dama da za su taimaka miki wurin fahimtar inda yaronki ya dosa.Wadannan abubuwa na da matukar muhimmanci ki lura da su da kyau domin ki gane irin aikin da za ki yi akansa.Ga wadansu daga cikinsu:
Karya: Ita wannan dabi’a ta kan ginu ne a jikin yaro sau dayawa dangane da yadda aka gina rayuwar shi a kai. Dole ne ki raba shi da karyar, ya zama mai sha’awar fadar gaskiya a duk inda ya ke kuma a cikin kowane lokaci. Idan ki ka kula da cewar ya cika surutu barkatai, da fadi-ba-a-tambayeka ba, da saurin kawo mi ki rahoto game da abubuwan da ba su shafeshiko ke ba, to alama ce Allah ya sa miki ki gane cewa zai iya zama makaryaci.Hakanan sai kin yi kokarin dabi’antuwa da yin gaskiya, kin gujewa fadar karya ke ma.Ki yabeshi matuka sannan ki yi mi shi kyauta duk lokacin da ki ka ji ya fadi gaskiya.
Almubazzaranci Da Rowa:Daga lokacin da ki ka kula da danki, kullum idan aka siya mai takalmi sai ya bace, to alamace Allah ya saka mikina ki tashi ki yi mai saiti domin idan ya girma a hakan,zai iya zama mutum mai almubazzaranci. Hakazalika Idan ki ka kula da cewar idan aka siya mai takalmi sai ya dade matukar dadewa yana kaffa-kaffa da shi, bai bace ba, to wannan wata alama ce Allah s.w.a ya saka miki ta ki gane lallai sai kin yi aiki akan shi idan bahaka ba zai girma ya zama makawali ko marowaci. Saboda haka aikin da yake akanki shine ki ga ya samu daidaito a wannan.
Sokonci Da Zalunci: Sannan kuma daga lokacin da ki ka kula da cewar danki idan ya shiga cikin yara yana wasa sai ya yi ta rabe-rabe, wannan ya doke shi, wancan ya dokeshi, to lallai wannan yana nuna alamar idan bata yi aiki akan shi ba ya girma al’umma ba za ta amfana da shi ba. Sannan ki lura da kyau cewar idan ki ka ga yaro yana cin gaban dan’uwansa a lokacin da su ke cin abinci, ko kuma yana wawaso ko tattara abincin a gabansa ya fi na gaban dan’uwansa yawa, to ya zama mai hadama kenan, sai an yi aiki babba a nan ma. Hakazalika ko ki ka kula da cewar da ya shiga cikin yara zai yi wasa sai a ji yaran sun fara kuka, to lallai sai kin yi aiki akanshi kada ya girma ya zama azzalumi.
Fushi: Masu iya Magana suna cewa “hakuri shi ne maganin zaman duniya”. A wani lokacin kina iya kula da cewa danki ba shi da hakuri da afuwa ga duk wanda ya kuskura ya taba shi. Ko dai ya yi zagi ko kuma ya kai duka. To hakan alama ce Allah ya sa miki ki gane cewa idan ba ki yi aiki a kanshi ba zai iya kasaita da halayya ta fushi a lokacin da ya girma, wanda hakan yana iya janyo aika-aika da danasani, kamar raunata wani ko kuma wani lokacin ma kisan kai.
Maye :Daga lokacin da yaronki ya fara tasawa, wajibi ne ki saka ido sosai ki ga irin abokan da ya ke yin mu’amala da su domin ki iya tantance mishi abokan da za su iya taimakon rayuwarsa da wadan da za su iya illatar da tarbiyyar da ki ka yi ta ginawa shekara da shekaru. Za ki yi kokarin yin hakan ne ta hanyar ba shi shawara da kuma yi mishi izina da wadansu misalai da ba za a rasa ba a kewaye da ku.
Hakika akwai shekarun da ba zai yiwu ki cigaba da yi wa danki fada ba kamar lokacin da ya ke karami ba, musamman idan ya kai lokacin samartaka. Abin da ya fi a gareki daishi ne kusanto da shi zuwa gareki ta hanyan jawoshi a jiki da dabarun nuna mishi kauna da damuwa da duk abinda ya shafe shi. Babbar hanyar kuwa da za ta taimakeki ki cimma nasara it ace, Ki sa shi ya aminta da ke sosai.
Raini Da Girman Kai: Za ki ji dadi kwarai idan ki ka ga danki ya iya saukar da kai da girmama na gaba da shi. To idan kuwa ki ka ga sabanin hakan tare da shi, ba ki yi aikin da ya dace da ke ba ne.Ki lura kwarai da cewar duk lokacin da ki ka kula yaro bai damu da gaishe da nagaba da shi ba ko kuma ba ya sassauta murya a lokacin da ya ke yin magana da manya,sannanba ya nutsuwa ya saurari maganar da ake yi da shi,to wannan alamace da ta ke nuna miki cewa idan ba ki yi aiki akan shi ba sai ya girma ya zama mai raini da girman kai.