- Girman Kai Ne Ko Cigaban Sarkin Baka?
Kamar yadda ya gabata, an bayyana irin sana’o’in gargajiya suke a kasar Hausa, cewa, kowane gida a kasar Hausa yana gudanar da wata sana’a daga cikin sana’o’in gargajiya na Hausawa, kuma suna koya wa ‘ya’yansu don su sami abin dogaro da kai, a wannan zamani al’amarin ya sauya. Dalili kuwa shi ne, shigowar zamani da shigowar Turawan Mulkin mallaka da kawo ilimin zamani da suka yi wanda ya haifar da samuwar ayyuka a ma’aikatun gwamnati da kamfanoni ya sa matasan kasar Hausa yin watsi da sana’o’in gargajiya da suka gada suka fifita ire-iren wadannan ayyuka kan wadannan sana’o’in
Da tafiya ta tafi, sai aka sami karuwar ‘yan makaranta wadanda suka kammala karatun sakandare da na gaba da sakandare da na jami’o’i. A gefe guda ga matasa kodai suna gani sun yi karatun boko sun cigaba, irin na sarkin baka, yana dada shiga jeji, yana ganin ya cigaba, ko kuma girman kai da zarmiya ne yake damunsu suna ganin sun fi karfin irin wadannan sana’o’in, ko kuma yaushe za a tara kudi da irinsu?
Sannan ga damammaki a gwamnati da kamfaninka sai raguwa, don haka, sai ma rage ma’aikata a kamfannunka, wannan ne ya sa wasu matasan suka koma bangar siyasa, ‘yan mata suka shiga karuwanci, kai wasu ma sai suka kama sace-sace da fashi da makami da ta’addanci. Abin kunya za ka iske daga cikin ire-iren wadannan matasa akwai wadanda suka kware a daya daga cikin wadannan sana’o’i, amma saboda bai tsaya ya koya ba idan za ka zaunar da shi ka ce ya bayyana maka ire-iren kayayyakin da ake amfani da su wajen yin wannan sana’a ba ma yadda ake yin wannan sana’a ba, ba zai iya ba, sai dai ya yi ta ‘yan kame-kame. Wannan ba karamin kalubale ne ba ga matasan Hausawa a wannan zamani.
Dangane da wannan al’amari matukar muna son mutuncinmu da arzikinmu da daukakar da Allah Ya yi al’ummar Hausawa ya dawo yadda za mu sami cigaba mai dorewa dole ne mu koma wa sana’o’inmu na gargajiya, mu yi amfani da ilimin zamani da muka koya mu haɓaka su yadda za su tafi daidai da zamani.
Shawara ga magada sana’o’in gargajiya na Hausawa.
- Wanzamai, a yau ya kamata su fadada tunaninsu domin zamani ya tafi da su, alal misali, a gargajiyance, aikin wanzamai shi ne aski, cire beli, yi wa yara kaciya, da bayar da magunguna. A yau tunda zamani ya canza, me zai hana su zamanantar da sana’ar tasu ta yi daidai da zamani, amma sun bar ‘yan kutse sun kwace suna so su yi mata gata, su kuma an bar su ba tsuntsu ba tarkon, kuma bawan ba kanin, kai za mu iya cewa sun yi biyu-biyu, jifan gafiyar ɓaidu.
Kai idan ka zurfafa, ka iya cewa, kamata ya yi a ce, da karatun zamani ya a ce, ‘ya’yan wazamai ne suke cika tsangayar koyar da aikin Likitanci ko jinya ko hada magunguna a jimi’o’in kasar nan ko na waje domin tafiya da zamani. Kalubale a gare ku wanzamai, in ba ka tafi da zamani ba, zamani zai tafi ya barka.
Makera, kamar yadda muka sani, makera su ne suke kera kayan amfani gida, kamar su wukake da tukwane da kwanuka da ludaya, sannan su suke kera kayan kwalliya kamar su dankune da sarka da awarwaro da dai sauransu. A yau su ma sun yarda sana’arsu sun ce kodai dana waje za su rinka amfani, da a ce sun daure sun tafi da zamani da sun zamanatar da sana’arsu ko kuma da a ce a yau ‘ya’yan makera ne suka fi yawa a tsangayar koyar da kere-kere da abin ba haka zai zama ba.
Madora, kamar yadda muka sani, sana’ar dori sana’a ce ta dori idan mutum ya karye a kasar Hausa.