Binciken da masana suka yi, sun gano cewa babu abinda ya fi ta’azara a wannan lokacin kuma yake ciwa al’umma tuwo a kwarya kamar yi wa yara kananan fyade, sannan hukunci ba ya tasiri ga mafi yawan wadanda suke aikata wannan ta’asa.
Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da hukumomi da kungiyoyin kare hakkin yara na cikin gida da kuma na kasashen waje suke fafutukar ganin an kare hakkin yara musamman ta hanyar hukunta wadanda aka kama da laifin yi wa Kananan yara fyade.
Abu kamar wasa, sai kara yaduwa yake a cikin birni da karkara ta inda da wahala rana ta fito ta fadi baka ji labarin wani ya yi wa wata karamar yarinya fyade ba, ko kuma yana da wahalar gaske ka je kotu ba ka ga jami’an ‘yan sanda sun gabatar da wani da laifin yi wa yara kananan fyade ba.
Sai dai kuma wani abu da ke daure kai shi ne, ana daukar mataki abin yana cigaba da faruwa kamar wutar da ji, wani lokaci ma, za a kama mutun da wannan zargin maimakon ka ji cewa yana yi domin biyan bukatarsa sai ka tarar cewa wani boka ko matsafi ne ya ba shi sa’a ya yi lalata da karamar yarinya domin biyan bukatar duniya.
Kazalika a wani lokaci ma, sai ka ga cewa bayan an yi lalata da karamar yarinyar da ba ta san abinda duniya take ciki ba, a karshen sai a raba ta da rayuwarta domin gudun kar asiri ya tonu, wanda yanzu haka kungiyoyi sun dukufa wajen ganin wannan masifa ta yi sauki so sai.
Daga cikin kokarin da ake shi ne, wata Gidauniya a kasar Ingila ta kaddamar wata manhaja wadda za ta bawa al’umma damar bayar da rahoto kai tsaye lokacin da ake yunkurin aikata fyade.
Kungiyar Kula da Hakkin Kananan Yara ta Nijeriya, da hadin gwiwar Gidauniyar Jose daga kasar Turai, su ne suka kaddamar da wannan sabon ci gaba a wayoyin hannu kirar zamani musamman wanda aka fi sani da ‘Android’ wadda za ta tona asirin masu lalata da kananan yara ta hanyar APP “Stop CSE”
A tattaunawarsa da jaridar LEADERSHIP A Yau (Asabar) a Abuja, shugaban kungiyar ta Jose Foundation, Prince Martin Abhulimhem, ya bayyana cewa, gidauniyarsu ta APP na bakin cikin labaran da take ji yadda ake yin lalata da kananan yara a Nijeriya da ma wasu sassa na duniya baki daya.
Martin ya ci gaba da cewa tonon asirin da wannan manhaja za ta yi ga masu irin wannan mummunar dabi’a ta lalata da kananan yara, zai sa su shiga taitayinsu, ba kamar a lokutan baya ba da suke cin karensu babu babbaka, saboda kunya da al’adar da ake da ita ta rashin son tonon asirin iyali.
Sannan sai ya bukaci iyaye da yara da su sanya manhajar ta APP “StopCSE” a wayoyinsu, domin zai taimaka masu a matsayin hujja wajen neman hakkinsu a kotu.
Baya ga wannan akwai moriya da yawa da za a iya ci ta hanyar amfani da wannan sabuwar fasaha.
A karshe, Martin ya ce, kwananan za su shirya taron kara wa juna sani kan yadda za a yi amfani da wannan sabuwar manhaja, da ake fatan ta kawo karshen badala da kananan yara a dukkan duniya.
Sai dai har yanzu mutane musamman a karkara suna da karancin wayewar kai wajan kai rahotan ire-iren wadanna matsaloli zuwa ga wata kungiya ko hukuma mafi kusa domin daukar mataki musamman idan wanda ya aikata laifin wani babban mutun ne ko kuma dan wani ne.
Hakan yana taimakawa wajan cigaba da zaluntar kananan yaran da ba su ji ba su gani ba, wasu saboda rashin gata sai dai gobe kiyama wasu kuma kungiyoyin sa kai da na kare hakkin dan Adam da kuma ‘yan Jarida na taka mahimiyyar rawa domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu, inda a wasu lokuta ake samun nasara.
Wannan annoba dai tana neman gindin zama a jihar Katsina, inda ko a shekarar 2014 sai da aka samu rahotannin fyade guda 63 kuma kimanin 21 sun faru ne a cikin birnin Katsina kafin abin ya ta’azara daga baya.
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta samu rahotan fyade har guda 112 a jihar Katsina sannan ta yi nasarar gabatar da mutane 79 a gaban kuliya manta sabo domin fuskantar tuhumar ake yi masu.
Haka kuma akwai wasu matsalolin da suka shafi laifin fyade wanda sakaci ko rashin sanin hanyar da za a bi domin daukar matakin shari’a a hukumance ko a kungiyance yasa babu so a lissafin hukumomin tsaro.
A karamar hukumar Musawa ta jihar Katsina a watan Mayu na wannan shekarar ta 2017 an kama wani mutun mai suna Salisu Magaji dan shekaru 57 ya yi wa yarinya yar wata bakwai fyade wanda hakan ya yi sanadiyar rasa ranta, bayan an kwantar da ita a asibitin kula da yara da mata masu juna biyu na Turai Yar’adua da ke Katsina.
Haka kuma an kama wasu mutane biyu a garin unguwar Bawa da ke karamar hukumar Danja sun yi wa wata yarinya ‘yar shekara daya fyade bayan sun fizgeta daga hannun mahaifiyarta. A yayin da aka kama wani mai suna Abdul Bashir ya yi wa ‘yar shekara shida fyade, sannan ya shaidawa manema labarai cewa wani bokansa ya ya ce yi amfani da ita akan wata biyan bukatarsa ta duniya.
Kazalika a wannan watan da muke ciki rundunar ‘yan sanda sun gabatar da wani shugaban makarantar firamari (Headmaster) mai suna Sule Yusuf dan shekaru 57 a gaban kotu bisa zargin yin lalata da yaro namiji dan shekara hudu.
Wannan al’amari na faruwa fadar mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ta fitar da wata takardar sanarwa inda ta dakatar da shi daga sarautar magatakaradar Katsina.
Sakamakon yawaitar wannan matsala ta fyade ta sa bangaran shari’a a jihar Katsina suka dukufa wajan sabunta dokar nan da ta yi tana jin hukuncin shekaru goma sha hudu a gidan wakafi idan an kama mutun da laifin yin fyade sannan wanda aka kama da laifin zai biya tarar naira dubu hamsin ga iyalan wanda aka yi wa fyadan.
A cigaba da farautar masu wannan halayar rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina ta yi nasarar damke wani mutun mai suna Inusa Aliyu dan shekaru 30 da haihuwa a karamar hukumar Rimi ta jihar Katsina yana lalata da ‘yar cikinsa mai kimanin shekaru 14 Wannan lamari dai ya firgita jama’ar wannan gari tare da ba su mamakin faruwarsa, bayan da mahaifiyar yarinyar mai suna Mariya Inuwa ta kai rahotan faruwar lamari ga ofishin ‘yan sanda na karamar hukumar Rimi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina DSP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce tuni bincike ya yi nisa game da wannan batu kuma da zaran sun kammala za su mikashi gaban kuliya manta sabo domin fuskantar hukunci.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Katsina Usman Ali Abdullahi ya bayyanawa manema labarai cewa sun samu rahotan fyade har guda 111 a cikin shekarar da ta gabata 2016 daga bangarori daban-daban da jihar wanda acewarsa abu ne ya kamata anuna damuwa so sai.
Usman Ali Abdullahi yana magana ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Katsina inda ya ce wannan bala’I ya wuce tunanin jami’an tsaro dole sai malaman addini da masu ruwa da tsaki sun shiga wannan batun kafin a kawo karshensa.
Tuni dai gwamnatin Katsina ta kana kwamiti wanda tsohon babban Alkalin Jihar Katsina, mai shari’a Sadik Abdullahi Mahuta ya jagoranta, kuma sun kammala aikinsu inda suka mika rahotansu ga ma’aikatar harkokin mata ta jihar Katsina tare da hadin gwiwar asusun kula da kananan yara na UNICEF.
Da yake karin haske game da abubuwan da rahotan na su ya kunsa mai shari’a Sadik Mahuta ya ce sai da suka yi la’akari da yanayin al’ada da kuma addini sannan, sun gayyaci duk wani mai ruwa da tsaki cikin batun dan a samu adalci ga kowa.
Suma sarakunan Katsina da Daura Mai Martaba Alhaji Abdulmumini Kabir Usman da Alhaji Umar Faruk Umar sun nuna goyan baya dari bisa dari game da wanna yunkurin gwamnatin jihar Katsina na kare hakkin yara ta hanyar kafa wannan doka.
A bangaran majalisar dokokin jihar Katsina kuwa mataimakin shugaban majalisar Dalhatu Usman Tafoki ya bada tabbacin cewa za su yi sud mai yi wa wajan ganin wannan dokar ta yi aikin yadda ya kamata musamman wajan kare hakkin yara kanana.
Baya ga wannan, shi ma shugaban gammayar kungiyoyin ‘yan sa iso a jihar Katsina kwamarad Bashir Usman Ruwan Godiya ya bayyana cewa ya kamata gwamnati ta bi kadin sauran shari’o’in da ake yi wa wadanda ake zargin da aikata laifin fyada kuma a tabbatar an yi adalcin wajan yin hukunci.
A cewarsa wannan zai taimaka matuka gaya, sannan zai zama izna ga mai shiri ko kokarin aikata laifi makamancin irin wannan, saboda a ganinsa rashin hukunta wadanda suka aikata laifin kamar wata dama ce ake ba wadanda suke son aikawa.