Kama Almajiran Sheikh Dahiru Bauchi Bai Dace Ba – Sa’id Bin Usman 

Almajiran

Tun bayan kama almajiran Sheikh Dahiru Usman Bauchi da gwamnatin Kaduna ta yi a makon da ya gabata, wannan ya ja cece-kuce a fadin Nijeriya da waje. Kungiyoyi da malamai, musamman almajiraI da daidaikun mutane sun yi fa tofa albarkacin bakinsu. Ganin haka ne Wakilin LEADERSHIP A YAU, HARUNA AKARADA, ya sami tattaunawa da mai rajin kare hakkin dan Adam wato shugaban kungiyar Internaonal Human Rigihts Today na kasa, MALAM SA’ID BIN USMAN, dangane da halin da kasa ta ke ciki, game da kama almajiran Sheikh Dahiru Usman Bauchi da cigaba da tsare Sheikh El-Zakzaki da kokarin gwamnoni na rancen kudin ‘yan fansho da wasu abubuwa da dama. Ga dai yadda hirar ta kasance:

 

Za mu fara da halin da ake ciki a garin Kaduna, a kwanakin baya ne tawagar Jami’an tsaro suka kwashe almajiran sheikh Dahiru Usman Bauchi a garin Kaduna, a matsayinku na hukumar kare hakkin dan’Adam wane mataki zaku dauka domin ganin wannan yara sun samu yanci?

To, ka san yanayi na rayuwa akwai wasu mutane domin a wannan lokacin akwai matsalalolin da suka dame mu, matsalar tsaro musamman ma a Jihar Kaduna ya kamata a ce ita gwamnati a nan bangaren ta mai da hankalinta ba wannan ba domin mutane su sami kwanciyar hankali ga matsalaloli nan kala-kala na barayin shanu ko masu garkuwa da mutane, ya kamata a ce gwamnatin Kaduna a nan ta mai da hankalinta, shi ne abin da ya kamata ta yi ba wai a je a kwashe mutane kawai kuma suna da ‘yanci ko ‘yan ina ne doka ta basu damar su zauna a ko’ina, suna karatun addini kuma ko kirista ne babu dalilin kama shi saboda haka wannan kuskure ne a je a sami daliban addini a kwashe su babu wani dalili mai kwari kuma ko ba karatun addini su ke ba doka ta basu damar zama a ko ina, yaushe za a je a tarkata su, na farko an firgitasu don haka wannan cin zarafi ne don haka muna jajanta musu.

 

A matsayin ku na hukumar kare hakkin dan Adam wane mataki za a dauka domin warware wannan matsalar?

Gaskiya ne, a 18 ga watan daya mun rubutawa gwamnatin Jihar Kaduna takarda cewa gwamna ya saki daliban Sheikh Dahiru Usman Bauchi, da ya kama domin kin hakan tauye musu hakkin su ne shi ma ba zai so hakan ta faru da shi ba idan ya ki jin wannan kiran to za mu gurfanar da shi a gaban kotu domin da mu da gwamnatin muna kasan doka ne don haka wannan abin ya sabawa doka a zahirance da badinan ce.

 

Za ku dau matakin Shari‘a ne ko ya ya za ku yi? 

Eh shi ne matakin karshe da za mu kauka amma muna fatan kafin haka ma ya ji wannan kiran da mu kai masa to ya hutasshemu ya saki mutanan da basu ji ba basu gani ba domin babu wanda ya fi karfin kuskure su kyale su kuma gwamnatin ta nemi afuwar wannan yara da al’ummar da aka zalunta wannan shi ne gaskiyar magana.

 

Ana fama da cutar Korona baka ganin wannan dalilan ne ya ja haka?

Ai tara almajirai ba shi ne zai kawo cutar Korona, ba wani almajiri da aka samu da ita zuwa yanzu ko makarantar boko ko ta addini waye wanda ta kama, Allah ya kare su daga gare ta kuma kwashe wannan yara ba shi ne zai sa cutar ta bar kasa ba domin abin a hannu Allah ya ke.

 

Shin kun yi magana da gwamnatin tarayya domin kawo karshen takaddamar? 

To wane Malami ne wanda ya yi suna a duniya kuma babu inda ba almajiransa wannan kame-kamen su ma akwai almajirai a cikinsu, amma yanzu fa to wannan da aka zo aka kama Allah kadai ya san nan gaba me wannan yaran za su zama shi ne gaskiyar Magana, sannan maganar sanar da gwamnatin tarayya ba zai yiwu ba a ce gwamnatin bata sani ba domin abu ne da kowa ya ji ba ma so abin ya ci gaba domin kada wani gwamnan ma gigi ya dauke shi ya aiwatar da irin wannan.

 

Akwai jagoran ‘yan shi’a Sheikh Ibirahim Zakzaki da gwamnati take tsare da shi tsawon shekara fiye da biyar ga shari’arsa taki gaba taki baya a matsayinku na hukumar kare hakkin dan Adam ay a kuke kallon wannan shari’a? 

Gaskiya wannan lamari ne mara dadi wannan abin ya faru ne a 2015 a garin Zaria, wato abin da zance a kan wannan shi ne na sami kwarin gwiwa ne dangane da irin wannan abubuwa da suke faruwa a kasar nan na rashin tausayi akan kowa to wannan abin gaskiya ya da aka yi ya sabawa duk wata doka ta kasar nan, amma duk irin wannan babu mamaki domin shi Sheikh Zakzaki ya gamu da jarabawa ce ta fuskar addini kenan domin komai ka ke yi za a gwada ka wannan shi ne. Na yi magana ne a mahanga ta addini, sannan kuma ni ba ina magana da yawun addinin Musulunci bane ko kirista ba a’a kamar tsare shi Sheikh Zakzaki to zan yi magana a matsayinsa na dan Adam wannan kuwa ko kirista ne ko Musulmi ne muna maganar dan’Adam ne kawai kuma wannan tsare shi da gwamnati ta yi ya sabawa sashe na 34 da sashe na 35 da ya ke cikin kundin mulkin kasa wannan kuskure ne an tauye masa ‘yancinsa na dan Adam. Domin duk abin da ya faru akwai mafita a doka tun farko ba a bi abin bisa doka ba a ki sakin sa wannan kuwa an tauye masa ‘yancinsa na dan Adam don haka ina kira ga gwamnatin tarayya da ta dubi Allah ta duba halin da kasa ta ke ciki ta saki wannan bawan Allah, shi ma ya shaki iskar yanci, domin dan’Adam ne shi kamar yadda shugabannin gwamnati suke su ma dan Adam. INTERNAONAL HUMAN RIGIHTS TODAY ta ce shi ma a sake shi.

 

Idan muka koma abin da ya shafi ‘yan fansho ana zargin gwamnoni zasu ranci kudinsu ya ya ka kalli wannan tsarin? 

Gaskiya wannan kuskure ne wannan kudin fa masu amfanar sa marayu da wanda suka bar aiki duk da haka baya isar wani ma gaskiya kwashe wannan kudin da sunan za a sa mutane cikin wani hali masu kokarin kwasar kudin fa gwamnoni ne kuma dukkan su Allah ya yi musu rufin asiri ga shawara idan har sun matsu sai sun ara akwai sanatoci da ‘yan majalisa su ara a nan ma domin in ka ari na nakasassu su yanzu bashin da ke kansu ma yayi wa

Idan suka dage sai sunyi yaya zakuyi ? Za mu nema mu ga hakan ba ta faru ba.

Exit mobile version