Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home MANYAN LABARAI

An Kama Mai Sayar Da Mushe A Bauchi

by Tayo Adelaja
September 21, 2017
in MANYAN LABARAI
2 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

A jiya Laraba 19 ga Satumbar 2017, ’yan sintiri masu aikin sa-kai don taimakon al’umma wadanda aka fi sani da ’yan kwamitin unguwar Bakin Kura suka yi nasarar cafke wani matashi dan kimanin shekaru 30, wanda ke safaran naman matacciyar dabba (mushe) yana sayar wa da jama’a a matsayin nama mai kyau.

samndaads

Matashin mai suna Safiyanu Aminu dubunsa ta cika ne a unguwar ‘Igbo Kuarters’ a lokacin da yake kokarin sarrafa naman domin sayar wa mabukata a matsayin halastaccen nama.

Dalhatu gambo Bakin kura yana daya daga cikin ’yan kwamitin da suka samu nasarar tasa kyeyar matashin daga inda yake aikata aika-aikar tasa zuwa gaban hukuma. Inda ya shaida wa LEADERSHIP A Yau yadda suka samu nasarar kamo mai mugun halin.

Ya ci gaba da cewa “da muka zo da shi ne muka nemi mahauta da su zo domin su gani ko membansu ne, inda suka shaida mana cewar basu da alaka da shi”. In ji sa

Dan kwamitin ya ce da suka tsaurara bincike a kan matshin sun iya fahimtar ya jima yana nemo naman mushe domin saidawa ga jama’a inda ya ce sun tabbatar ba mahauci bane “da muka yi bincike muka ce masa ya fada mana gaskiya, sai ya ce mana gaskiya wallahi tallahi ya tsintane ya dauko domin saida”. In ji sa

Ya ce daga bisani ne kuma suka hannanta matashin ga ‘yan sanda domin ci gaba da gudanar da bincike a kansa.

Wanda ake zargin Safiyanu Aminu, ya amince da laifinsa amma ya nemi gafarar jama’a kan wannan laifin nasa, sai ya bayyana hakan da sharrin shaidan ne, inda ya nuna cewar ba zai sake aikatawa ba. ya kuma shaida hakan ne a zantawarsa da wasu ‘yan jarida kafin a mika shi ga ‘yan sanda.

Shugaban kungiyar mahauta na karamar hukumar Bauchi Baba Uba ya bayyana matukar jin dadinda kuma farin cikinsu a bisa wannan nasarar da aka samu na kame mai aikata wannan laifin da ‘yan kwamitin suka yi, sai ya jinjina musu kan wannan aikin nasu.

Shugaban mahautan ya bayyana cewar har zuwa yau basu taba samun wani membansu mai cikakken rijista da makamancin wannan halin ba. sai ya shaida cewar mambobinsu na kungiyar mahauta suna nan suna ci gaba da nuna halin kyarai da kuma bin dokokin saida nama a kowani lokaci.

A bisa haka ne ya kirayi masu sayen naman da suke matukar kulawa da sanya ido wajen sayen naman. Kana ya sha alwashin ci gaba da farauto ‘yan bunburutu masu shafa musu bakin fenti a jihar.

SendShareTweetShare
Previous Post

Jam’iyyar PDP Ta Fara Canza Salo A Katsina

Next Post

An Kama Shi Da Tufafin Mata Da Daddare

RelatedPosts

Shugabannin Tsaro

Me Saukar Shugabannin Tsaron Nijeriya Ke Nufi?

by Muhammad
1 day ago
0

Sauka Suka Yi Don Kashin Kansu – Fadar Shugaban Kasa...

Zakzaky

Korona: Ku Mika Matar Sheikh El-Zakzaky Cibiyar Killacewa

by Muhammad
2 days ago
0

–Umarnin Kotu Ga Gidan Yarin Kaduna Daga Rabiu Ali Indabawa,...

Rigakafi

Korona: Jiga-jigan Nijeriya Na Sulale Wa Waje Amsar Rigakafi

by Muhammad
3 days ago
0

Daga Khalid Idris Doya, Biyo bayan sake bullar annobar Korona...

Next Post

An Kama Shi Da Tufafin Mata Da Daddare

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version