Kamaru Usman Zai Kawo Wasan Boxing Nijeriya

Kamaru

Shahareren dan wasan damben Boxing na duniya ajin mai biye da na tsaka-tsakar nauyi, Kamaru Usman mai rike da kambun ajinsa na UFC, na ziyara a Najeriya kasar sa ta asali karon farko cikin shekaru 26, inda ya ce zai kawo wasan nahiyar Afirka masamman nan Nijeriya.

Usman, wanda  ba a doke shi ba a wasanni 18, gami da nasarori 14 a jere, ya gana da manema labarai a birnin Legas ranar Lahadi, inda ya bayyana musu cewa, ako da yaushe gabanin soma fafatawa sai ya ji fargaba cikin zuciyarsa, amma kuma sai ya samu nasara.

Matashin mai shekaru 33, wanda shine dan Afirka na farko a tarihin UFC, ya ce yana shirin kawo wasannin UFC zuwa Afirka, bayan da Nahiyar ta samar da irinsa guda uku a zakarun gasar.

Ya yin da Usman ya kasance zakara a rukunin masu biye da tsakatsakan nauyi, Israel Adesanya shima dan Najeriya shi ne zakaran matsakaita nauyi sai kuma Francis Ngannou na Kamaru wanda ke zakaran ajin masu nauyi.

Gasar Turai: Za’a Tsaurara Matakan Korona A Birnin Saint Petersburg

Mahukunta a birnin Saint Petersburg, wadanda ke shirin karbar  bakuncin wasu jerin wasannin gasar Euro 2020, sun bayyana matakin kara tsaurara matakan hana yaduwar cutar corona a kokarinsu na dakile bazuwar cutar.

Jami’ai a birnin, birni na biyu da cutar tafi yiwa illa a kasar Rasha baya ga Moscow da ake sa ran za ta karbi dubban magoya bayan kwallan kafa daga Turai, sun bayyana daukar dukkan matakan da suka dace domin kare magoya baya da ‘yan wasa a lokacin wasannin na kwallon kafa mafi girma a nahiyar Turai.

Matakan da za’a dauka

Cikin matakan da aka dauka, daga ranar Alhamis gidajen abinci da wuraren wasan yara a manyan kantuna zasu kasance a rufe, sannan za’a hana sayar da abinci a bangaren ‘yan kallo da magoya baya.

Kazalika gidajen Cinema zasu rage ‘yan kallo zuwa kashi 50 cikin dari, kasa da kashi 75 da suke dauka yanzu haka, kuma za a rufe gidajen abinci tsakanin karfe biyu na safe da kuma 6 na safe.

Exit mobile version