Connect with us

DAUSAYIN MUSULUNCI

Kame Kai Daga Abubuwan Da Ba Su Dace Ba Ga Mai Azumi

Published

on

Da farko muna gode wa Allah mai rahama mai jinkai wanda bisa falalarsa da zabinsa ya yi mu ‘Yan Adam kuma a cikin Musulunci wanda shi ne addinin da Allah bai yarda da kowanne ba sai shi. “Addini a wurin Allah shi ne musulunci” kamar yadda ya zo a cikin Suratu Ali Imran.

Shi Musulunci an kafa shi ne a kan rukani guda biyar. Na daya ita ce La’ilaha illallahu Muhammadur Rasulullah SAW (Tauhid), wannan ne Musuluncin ma baki daya domin idan mutum bai da ita, to ko ya yi Sallah da Azumi da Zakkah da Hajji ya yi a banza, Allah ba zai karba ba tunda babu Tauhidi a ciki. Amma da mutum zai shiga Musulunci bayan ya fadi La’ilaha illallahu nan take sai ya kasance ya mutu ba tare da ya samu ya yi sauran ibadu ba zai shiga Aljanna. Sallah ita ce rukuni na biyu, sai Zakkah na uku, sannan Azumi na hudu da kuma Hajji na biyar.

To a wannan watan ne muke ba da rukuni na uku na Musulunci. Idan watan ya zo Manzon Allah (SAW) yakan yi bishararsa kuma ya hori Muminai su wanke zuciyoyinsu a yi shirin gyara. Yana daga cikin Hadisin Jibrilu Annabi (SAW) zai hau mumbari sai aka ji ya ce “amin” da ya taka matakala ta farko, da ya sake taka ta biyu ma ya ce “amin”, haka nan ta uku. A ciki aka tambaye shi menene amin din da ya ce? Sai Manzon Allah (SAW) ya ce “Jibrilu ya ce mun wanda ya riski iyayensa biyu ya ki yi musu alherin da zai basu dadi har su sa masa albarka ya shiga Aljanna; to idan Allah ya sa shi a wuta ya danna shi a can ciki shi ne na ce amin. Kuma Jibrilu ya kara ce mun wanda ya riski Ramadan bai yi abin da Allah zai gafarta masa a ciki ba idan Allah ya sa shi a wuta ya danna shi a can ciki shi ne na ce amin”.

Wannan Hadisi yana nuna mana cewa babban abin da ake so idan Ramadan ya shiga ba wai muradi kawai a ji yunwa; a ji kishin ruwa ba, a’a, a yi kyakkyawan aiki, a wanke zuciya a gayara halaye yanda Allah Ta’ala zai gafarta mana. Ita gafara ma’anarta ita ce ka yi laifi an yafe, to akwai sauran falaloli kuma. Koda an yafe maka ka shiga Aljanna ba shikenan ba, domin ita Aljanna tana da martabobi (hawan-hawa). Akwai ma abin da ya fi Aljanna dadi shi ne “Yardar Allah”, akwai abin da duk ya fi wadannan kuma shi ne “Ganin Allah Ta’ala”.

Idan mutum yana son wannan, wajibi ne ya kyautata ibadu, ya rika yin abubuwan da za a hauhawar da shi darajoji da martabobi kamar yadda Allah (SWT) ya saukar, Manzon Allah (SAW) ya bayyana, su kuma Malamai suke koyar da mu. Mu yi murna ‘yan’uwa Musulmi saboda watan Azumi wata ne mai girma kwarai da gaske. Kyauta ce ga Al’ummar Manzon Allah (SAW) wadda rayuwarmu ba ta da yawan shekaru musamman idan aka kwatanta da al’ummon baya. Misali, Adawa mutanen Annabi Hudu (AS) sai mutum ya kai shekara 500 sannan ne zai balaga a cikinsu. Mu kuwa kwata-kwata kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya ce, shekarunmu 60 ne ko 70, ‘yan kadan ne suke zarce hakan. To amma albarkar wannan al’ummar ta fi ta wadannan masu dimbin shekarun saboda maigidan namu Manzon Allah (SAW). Allah ya ba mu daren Lailatul Kadri a cikin wannan watan wanda ya fi wata 1000, kimanin shekara 83 da ‘yan watanni. Duk shekara idan mutum ya yi ibada a ciki za a bashi ladan kamar ya yi shekara 83 yana ibada kuma a cikin shekarun babu sabo duka zalla ibada ne a ciki. Ka ga a duk Ramadan Musulmi muna da safayar shekara 83. Wanda ya riski Ramadan ya yi ibada a daren Lailatul Kadri sau 40 misali, yana da ladan shekara 83 sau 40, idan aka buga lissafi zai zama yana da shekarar ibada zalla dubu uku da dari uku da ashirin (3,320). Wannan falalar Allah ne. Don haka wajibi ne mu gode wa Allah da ya ba mu Ramadan kuma mu kara godiya da watan ya kama muna cikin rayayyu masu azumtar watan. Za mu kawo bayanai daidai gwargwado kan hukunce-hukunce da kuma falolin da ke cikin watan sannu a hankali insha Allahu.

Azumi ba yana bukatar kame kai daga barin ci da sha da saduwa da iyali da rana ba ne kawai, wajibi idan mutum yana so ya samu cikakken ladansa sai ya kiyaye aikata dukkan abubuwan da ba su kamata ba.

Abu Huraira (RA) ya ruwaito Hadisi daga Manzon Allah (SAW) cewa “Azumi ba yana nufin a bar ci a bar sha ba ne kawai, ya hada har da barin zantukan banza, da batsa. Idan wani ya zage ka ko ya yi maka wauta, ka ce ma sa ni mai azumi ne, ni mai azumi ne.”

A wani Hadisin kuma, Manzon Allah (SAW) ya ce “Duk (mai azumin) da bai bar gulma da aiki da gulmar ba, Allah bai damu (mai yin haka) ya ci abinci; ya sha abin sha ba.” Ma’ana dai Allah bai damu da azumin nasa ba.

Har ila yau a wani Hadisin, Annabi (SAW) ya ce “Da yawa mai azumi bai da komai (na lada) sai yunwa, da yawa mai sallar dare ba shi da komai (na lada) sai rashin barci.” Ma’ana sun sha wahalar banza kenan babu lada a ciki.

Ya ku jama’ar Musulmi ya kamata mu kiyaye. Babu kyau da mutum ya ji wata ‘yar magana ‘yar kadan sai ya kama ya yi ta yadawa a gari yana bata tsakanin mutane. Yin haka gulma ce sosai.

Don haka wajibi ne mu kiyaye kawunamu daga aikata dukkan nau’o’in abubuwa marasa kyau na ashar, da zage-zage da cin mutuncin jama’a.

Niyya da sahur da buda baki rukunai ne masu muhimmanci na azumi. Niyya wajiba ce, idan aka yi azumi ba tare da ita ba azumi ya baci. Sahur da buda baki sunnoni ne masu karfi, don haka ga takaitaccen bayani a kan ko wannensu daga Hadisan Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad (SAW).

Hadisi ya zo daga Matar Annabi (SAW), Sayyida Hafsatu cewa, Manzon Allah (SAW) ya ce “Wanda bai yi niyya da dare ba kafin fitowar Alfijir ba shi da azumi.” Magana a kan niyya kenan. Amma kuma akwai wasu malamai da suke ganin idan Azumin nafila mutum zai yi, zai iya yin niyya koda gari ya waye, wasu kuma suka ce hadisin ya game Azumin nafila da na farilla baki daya.

A nan wurin, mu a Nijeriya akwai wadanda suke kiran asalatu a cikin dare tun kafin fitowar Alfijir (wanda babu inda ake yin haka a duk kasashen Musulmin duniya idan ba a Nijeriya ba), to mutum ko ya ji wannan zai iya yin niyyarsa. Amma idan ya ji masu kiran sallah sun fadi assalatu a kiran sallah na biyu wanda daga hakan sai yin sallah, to lokacin yin niyya ya kure.

Dangane da batun Sahur kuwa, an karbo hadisi daga Anas bin Malik cewa Annabi (SAW) ya ce “Ku rika yin Sahur domin akwai albarka a cikinsa.”

Mutumin da ba ya yin Sahur ba zai sami wannan falalar ba matukar ba wani uzuri ne na shari’a ya hana shi yi ba. Don haka ba birgewa ba ne yadda wasu ke gadara da cewa suna yin azumi ba tare da Sahur ba. Akalla koda ruwa ne mutum ya yi kokari ya tashi ya sha.

Sannan an fi so a jinkirta Sahur bisa dogaro da hadisin Abu Zarrul Gifari da ya ce Annabi (SAW) ya ce “Al’ummata ba za ta gushe ba cikin alkhairi idan suna gaggauta buda baki da jinkirta Sahur.”

Amru bin Maimuni ya ce “Sahabban Manzon Allah (SAW) sun kasance mafi gaggawan mutane wajen yin buda baki kuma su ne mafi jinkirin yin Sahur.”

A kan buda baki kuma, an samo hadisi daga Sahlu bin Sa’adu (RA) Manzon Allah (SAW) ya ce “Mutane ba za su guje cikin alkhairi ba muddin sun gaggauta buda baki.” Wannan yana nuna mana cewa an fi so a gaggauta yin buda baki da zarar rana ta fadi. Ko ayar cikin Suratul Bakara da ta ce “A ciki azumi zuwa dare…” tana nufin faduwar rana ce domin da rana ta fadi dare ya yi kamar dai yadda idan Alfijir ya fito to gari ya waye.

Manzon Allah (SAW) yakan yi buda baki kafin Sallar Magrib. Galibi ya fi yin buda baki da danyen kayan marmari. Idan an samu iko sai a yi koyi da wannan Sunnar. Idan kuma ba a samu ba sai mutum ya yi da abin da ya sauwaka ma shi.

Ga addu’ar da Annabi (SAW) yake yi a lokacin buda baki “Allahumma lakas sumtu wa ala rizkika afadartu”.

Allah gare ka na yi wannan azumin (ma’ana don Allah ya yi azumin), kuma da arzikinka na yi buda baki.

Akwai wani kuma da ya zo da karin “Fagfirli ma kaddamtu wa ma akkhartu.” Ma’ana “Ka gafarta mun abin da na aikata da ya gabata da abin da na jinkirta.”

Yana da kyau a mutum ya rika yin addu’a a lokacin buda baki ta neman biyan bukata a wurin Allah (SWT) saboda addu’ar da aka yi a lokacin karbabbiya ce.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: