Abubakar Abba" />

Kamfani Zai Cigaba Da Tallafa Wa Kananan Manoman Masara A Nijeriya

kimiyyar zamani

Kamfanin Babbar Gona ya kashe sama da Naira biliyan shida a cikin shekaru tara a Nijeriya tare da bayar da bashi ga kananan manoma sama da 70,000 don su bunkasa noman su.

Manajin Daraktan kamfanin Mista Bukola Masha ne ya sanar da hakan bayan da kamfanin ya kammala wata ganwa kan dabarun noma na shekara-shekara.
Mista Masha ya ci gaba da cewa, sama da bashi 140,000 kamfanin ya rabarwa da manoman Masara da suka nioma kadada sama da 100,000 a jihohi biyar da ke Arewacin Nijeriya.
Ya ci gaba da cewa, jihohin su ne, Kano, Kaduna, Katsina, Bauchi da kuma Filato, inda ya kara da cewa, an kuma bai wa manoman bashin e don su habaka yin girbin su da kuma samarwa da kansu karin kudaden shiga.
Ya ce, ko da yake abinda kamfanin yafi mayar da hankali akai shine, fanin noman Masara da kuma yadda kamfanin zai taimaka wajen kara samar da damarmaki kan sauran amfanin gona.
Ya bayyana cewa, kamfanin ya na son akalla manoma miliyan daya su amfana da bashin nan da shekarar 2025.
Ya ce, abinda kamfanin yafi mayar da hankali akai shi ne, noman Masara, amma kamfanin yana kuma kara fito da wa su damarmaki kan sauran wasu amfanin gona.
Ya sanar da cewa, abinda kawai mu ke bukata daga gun manomi shi ne, gonarsa da kuma zagewa in har mun bayar da daukin a bangaren sanar kayan aikin noma na zamani, haro, ingantaccen Iri, takin zamani, da kuma magungunan kashe kwari da kuma ci gaba da bai wa manomi shawarwari.
Shi m a nasa jawabin, wani Darakta a kamfanin na BabbanGona Alhaji Bello Maccido ya yi nuni da cewa, Babban Gona an san shi a cikin Nijeriya da kuma a wasu kasashen duniya, mussmman saboda kokarins na bayar da tallafin bashi don yin noma, inda ya ke taimakawa kan tattalin arzikin kasa da ya kai kasi 29 a cikin dari.
Ya ce, kamfanin ya na kuma amfana da dauki daga wurin cibiyoyin kudi na kasa d kasa, inda ya kara da cewa, muna kuma yin dubi kan bayar da gudnmawa ga kara bunkasa tattalin arzikin Nijeriya wanda ya kai kimanin kashi 29 a cikin dari, inda ya yi nuni da cewa, domin munyi amannar hakan zai kara habaka noma da kuma bunkasa sana’ar manoman Nijeriya.
Ya sanar da cewa, hakan ne ya sanya muka ga ya zama wajibi mu bayar da taimakon, inda ya kara da cewa, ba wai kamfanin zuba jari na Nijeriya kawai bane ke taimakawa kamfanin BabbanGona ba, harda wasu cibiyoyin kudi manya na kasar waje.
Wani da ya amfana da shirin Malam Halliru Sale mazaunin Kaduna ya ce, noman zamani na bukatar a samu intantaccen irin , inda ya yi nuni da cewa kamfanin na BabbanGona ya tanadi hakan.
Ya ce, kafin zuwan kamfanin na BabbanGona, suna kawi tona kasar gonakan su ne kawai, amma ba noma su ba, amma wannan ita ce hanyar da ta da ce mu rungumi sabuwar dabarar yin noma, musamman don samun amfani mai ya wa.
Ita ma wata da ta amfana Uwagida Hajara Luka ta ce, da farko mun dan ja da baya, amma da mu ka gwada, munga shirin ya na da kyau, inda ta ce, a kalla ta na noma buhuhunan Masara takwas a rabin kadada, amma a yanzu, ta na noma akalla buhunhuna 25.

Exit mobile version