Connect with us

KASUWANCI

Kamfanin Aiteo Ya  Musanta Zargin  Hannun Sa A Zanga-zangar Da  Aka Yi Wa JTF A Neja Delta

Published

on

Mahukuntan kamfanin Aiteo dake hakowa da kuma sarrafawa ya nisanta kansa daga zanga-zangar da mazauna ‘yan yankin Nija Delta suka yiwa jami’an sintiri na  (JTF) suka yi a jihar.

Idan ba a manta ba a ranar juma’ar data gabata ce, mazauna yankin na Neja Delta suka kira taron manema labarai a  Abuja, inda suka bukaci da ayi bincike akan ayyukan na JTF da Adimiral Apochi Suleiman yake jagoranta.

A cikin sanarwar da da aka fitar kamfanin na Aiteo kalubalanci kwamandan shirin na   Operation Delta Safe, inda Admiral Suleiman, ya sanar da cewa, kamfanin da kuma babban jami’in sa Benedict Peters  ne hummul habali haba’insin janyowa ‘yan asalin jihar ta Nija suka rubuta koke a bisa abinda ya auku sakamakon aikin na JTF.

A cewar kamfanin, don a kaucewa dukkan wani kwankwanto, duk a yunkurin da  Adimiral Suleiman ya yi na cewar da hannun mu dumu- dumu akan shiga ayyukan wadanda suka hada taron, wata manufa ce da baza ayi nasara ba.

Kamfanin ya kalubalanci Adimiral Suleiman da ya mayar da martani akan zarge-zargen da masu zanga-zangar suka bijiro dasu, kamfanin ya kara da cewa, matsayar sa kokari ne don karkatar hankula da kuma nufin hada labaran karya don cimma wata burin sa.

Kamfanin ya ci gaba da cewa, Adimiral din ya gano akwai wani abu da aka yi ba daidai ba, inda hakan ya sabbaba mazuna yankin suka nemi a basu kariyar rayukan su a kasar su da dukiyoyin su da kuma kadarorin su ganin yadda satar mai ya yi kamari a yankin.

Kamfanin ya yi nuni da cewa, ga wanda aka dorawa nauyin kare rayuka da dukiyoyin mazauna yankin, amma sai gashi ‘yan yankin suna neman chanji.

Kamfanin ya yi nuni da cewa, idan aka yi la’a kari da yadda ake ake sarrafa mai a yankin a kullum da ya kai yawan 90,000, NNPC da Aiteo JB, a yanzu haka yana da nauyin samar da mai kashi biyar bisa dari a kasar.

Kamfanin ya kara da cewa, don yin hakan, ya dauki sama da daruruwan ma’aikata da kuma wasu dubban leburori aiki kai tsaye a bisa yarjejeniyar gudanar da aiki.

A cewar kamfanin, abin takaici mune aka fi yiwa satar mai a kasar nan, kuma dole a warware wannan maganar.

A cewar kamfaninn  Adimiral din yana yin nuni akan layin mai na Nembe Creek Trunk a matsayin kayan Benedict Peters, wannan kuma abun takaici ne.

A cewar kamfanin, NCTL yafi dacewa a danganta shi da kayan gwamnatin tarayya wanda mu abokan hadaka ne kawai.

Kamafanin ya yi nuni da cewa, NCTL kaddara ce NNPC, inda kamfanin Aiteo ya yi hadaka da NNPC, inda Aiteo ya mallaki kashi 45 bisa dari sai kuma gwamnatin tarayya ta mallaki kashi 55 bisa dari.

Kamafanin ya yi nuni da cewa, shin a ta ya ya ne Adimiral din zai bayyana cewar kaddarar ta bututun wasu ne suka mallake su?

Aiteo shi ne na uku da ake yiwa katsalandan akan layin sa na mai,inda aka ya janyo hujewar layin aka kuma dinga samun rufewa, inda dole aka dauki matakin gaggawa na yin gyara.

Har ila yau, hakan ya janyo mata rufewa  da kimanin kwanuka 145 da aka kiyasta ya kai anyi asarar ganga  miliyan 50.386 na danyen mai a cikin watan satumbar shekarar  2015.

A cewar kamfanin, a ranar 1 ga watan Mayun 2018, an gyara jimlar bututun mai guda 24.

kamfanin na Aiteo ya samu nasarar gyra bututan mai guda tara da aka fasa a cikin watan Mayun 2018 a cikin kudi masu tsada.

Kamfanin ya kuma koka akan satar mai ta harmtacciyar hanya, inda hakan ke yiwa tattalin arzikin kasa nakasu.

Kamfanin ya nuna damuwar sa akan illar lala cewar mai wanda yak shafar kiwon lafiyar mazauna yankin.

 

A cewar kamfanin mai makon a magan ce zarge-zargen da Adimiral Suleiman

ya bijoro dasu, wadanda kuma suka kara taimakawa akan zanga-zangar,

hakan ya nuna cewar yana son boye wata manufa.

Kamfanin ya yi nuni da cewar, wannan furucin nasa bai dace ba kuma zai iya shafar harkar tsaro na kasa, musamman ganin cewar, Aiteo da sauran sune suka fi jin jiki wajen yi masu satar mai.

A karshe Aiteo ya ce, Nijeriya baza ta iya jure irin wannan ba ganin yadda wasu masu ruwa da tsaki suke son kawo nakasu ga tattalin arzikin kasar.

 

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: