A satin da ya gabata ne shahararren kamfanin nan mai kera wayoyi na alfarma wato Apple, da ke kasar Amurka ya sanar da fito da wasu sabbin wayoyi guda biyu, wato iPhone D (10) da kuma iPhone 8, su dai wadannan wayoyin anyi su da sabbin fasahohi wanda hakan ya sa suka yi wa sauran takwarorinsu na iPhone 6 da 7 fintinkau.
iPhone D ta zo da wata fasaha ta yadda za a iya mata caji ba tare da an jona waya a jikinta ba (Wireless charging), sannan tana iya gane fuskar mai ita (Face detection) ta yadda da zarar ya kalli fuskar wayar zata bude, sannan ga kamarar daukar hoto mai hasken gaske, kuma dukkan gabanta na gilashi ne. Abin da ya bambanta ta da duk sauran wayoyi shi ne yadda ruwa baya mata wata illa ko da ta fadi ciki.
Su dai wadannan rukunin wayoyin an musu farashin farko, iPhone D za a iya samunta a Dala 1,000 kimanin 365,000 kenan a naira, a yayin da ita kuma iPhone 8 za a same ta a dala 822, daidai da 295,920 kenan a naira.