Connect with us

LABARAI

Kamfanin Chana Ya Tallafa Wa Gombe Da Kayan Yaki Da Korona

Published

on

Kwamitin yaki da cutar Korona a jihar Gombe ya samu karin tallafin kayan yaki da cutar daga wani kamfani ta kasar China wato ‘Ganan Construction Company’.

Da yake mika kyautar kayayyakin ga Shugaban kwamitin, Manajan Gudanarwa na kamfanin GCC, Mr xu Kan, ya shaida cewar kamfanin ta samar da tallafin ne domin bada nata gudunmawar kan agaza wa kokarin Gwamnatin jihar Gombe na yaki da annobar nan ta Korona da ta zama gama-gari.

Mista Kan ya yi amannar cewar a irin wannan lokacin da ake kan yakar cutar Korona, a cewar shi batun yaki da cutar aikin ne na hadaka da bangaren gwamnati hadi da kungiyoyi masu zaman kansu da daidaikun masu hali.

Kayayyakin da kamfanin Chana ta bada tallafin sun hada daga takunkumin rufe hanci da baki guda dubu 30,000, sunadarin wanke hannu ta Sanitizer guda dubu 4,800, da kuma kwantena guda 40 na fanfon feshi don tsaftace muhalli.

A jawabinsa Shugaban kwamitin yaki da Korona a jihar, Farfesa Muhammad Idris, ya gode wa kamfanin a bisa tallafin da suka kawo, yana basu tabbacin amfani da kayayyakin ta hanyoyin da suka dace don cimma manufar samar da tallafin.

Shugaban yayi amfani da wannan damar wajen neman jama’an jihar da su ci gaba da bin matakan kariyan kai daga cutar tare da mutunta dokoki da ka’idojin da hukumomi suka gindaya don cimma nasarar yaki da annobar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: