Daga Abubakar Abba
Ana kan tattaunawa tsakanin Kamfanoni Rukunonin Dangote na sarrafa Suminti da kuma Kamfanin sarrafa Suminti dake Afirka ta Kudu, domin kamfanin na Rukunonin Dangote, ya samu. karbar ragamar ci gaba da gudanar da kamfanin na Afirka ta Kudu.
Tuni dai, Kamfanin na Afirka ta Kudun, ya kaddamar da wani, sabon sanya hannun jari na kimanin naira Biliyan 9.2.
Manufar ta Kamfanin Rukunonin Dangote na sarrafa Suminti, ya nuna bukatarsa ta cigaba da, tafiyar da Kamfanin na Suminti na Afirka ta Kudu, don kara samar da kasuwar sayar da Suminti a Afrika ta Kudun, da kuma a kasuwanni dake makwabtaka da kasar ta Afirka ta Kudu.
A rahoton kudi na shekara, da ya kare a ranar 30 din watan Maris din shekarar 2017, ya nuna cewar, Kamfanin sarrafa Suminti na Sephaku ya samar da kudin shiga Biliyan R2.28 dai-dai da msalin Dalar Amurka ta miliyan (178 million dollars) a cikin shekarar 2016.
Wannan idan aka kwantata da Kamfanin Simintin na Afirka ta Kudu da yake samar da kudin shiga Biliyan R9.6 dai-dai da Dallar Amurka Miliyan ($748 ), kenan a cikin shekarar in 2016, wanda ya rubanya har sau hudu na Kamfanin Suminti na Sephaku.
Tabbas, Kamfanin Simintin na Dangote zai so ya mallaki babban Kamfanin Suminti na Afirka ta Kudu, ganin zai bude masa fage na hada-hadar kasuwancin Kamfanin Suminti na Sephaku in har ya samu amincewar masu fada aji wato mahukunta.