Abubakar Abba" />

Kamfanin Discos Ta Kasa Dawo Da Naira Biliyan 326 Na Wutar Data Sayar A Wata 10 – NBET

Kudade

Kamfanonin dake rabar da wutar lantarki Discos a fadin kasar nan, ya gaza dawo da jimlar naira biliyan 325.54 ga NBET na kudin wutar da ya sayar daga Janairu zuwa Okutobar 20180
Gwamnatin Tarayya ce ta mallaki sake sayen wutar lantarki mai yawa daga kamfanonin dake samar da wutar a karkashin yarjejeniyar sayen wutar da kuma rabar da ita ta hanyar kwangilolinn da aka baiwa Discos, inda shi kuma kamfanin yake rabarwa da masu amfani da wutar dake daukacin fadin kasar nan.
An baiwa Discos takardun biyan kudin har naira biliyan 459.67 a cikin watanni 10 sai dai, ya biya naira biliyan 134.13 ne kawai inda sauran naira biliyan 325.54 suka rage
A cikin watan Janairu kamfanonin Discos bakwai da suka hadada, Benin, Eko, Ibadan, Ikeja, Kaduna,
Kano da kuma Fatakwal basu turawa NBET komai ba.
Hukumar wutar lantaki ta kasa NERC a cikin rahoton ta na kwanan nan ta bayyana cewar, rashin dawo da kudin ga NBET ya auku ne saboda masu lura da kasuwa saboda karancin kudi da Discos suke fuskanta da kuma rashin inganta ka’idar biyan kudin.
Babban ci gaban da aka ssmu wajen tara kudin shiga sun hadada samar da tsarararrun mitoci ga masu amfani da mitocin.
Acewar rahoton, kalubalen da na dawo da kudin, ya haifar da babban kalubale ga hukumar, inda wannan yana daya daga cikin durwushewar fannin na ssmar da wutar.
Rashin dawo da kudin, ya janyowa NBET cikas na sauke nauyin da aka dora mata.
Don magance wannan matsalar, hukumar ta fara tsaurara matakanta akan Discos na rashin dawo da kudaden ga NBET da kuma MO.
A saboda hakan, hukumar ta fito da tsari don a tabbatar da ana bin ka’ida da kuma biyan kudin don amfanin wadanda suke a fannin.

Exit mobile version