Daga Idris Umar, Zariya
A ranar Juma’ar makon da ya gabata ne kamfanin magani na ‘Galico Habal International’ ya kawo dauki ga mutanen Zariya da kewaye. Inda ya bayar da tallafin magunguna tare da yin tasa-tasai ga al’ummar da suka hada yara da manya.
Babban Manajin Darakta na wannan kamfanin, mista Patrick Ocoye ya bayyanawa manena labarai makasudin kai wannan tallafi, a yayin da suka kaddamar da aikin baje kolin da suka fara a filin bayan makarantar firamare ta ‘Amina’ da ke garin Samaru, a karamar hukumar sabon gari, da ke Jihar Kaduna.
Mista Patrick ya ce; “Babban dalilinmu na zuwa don bayar da gudummawar mu ga mutane Zariya da kewaye shi ne, mutane da yawa suna da cututtuka a jikinsu, kuma basu da halin da zasu samu maganin da za su yi amfani dashi, don haka muka kuduri aniyar kawo masu magunguna masu kyau da saukin farashi. Tare da bayar da wasu kyaututtuka ga marasa galihu don taimakon al’ummar kasarmu baki daya. Kuma za mu ci gaba da bayar da wannan taimakon ga mutane har illa masha Allahu”
sun aunani da na’urar bature take suka bani magani kuma gashi yanzu ina gani tangaran. Baa bin da zan ce sai dai Allah ya saka da Alkairinsa”.
A yanzu haka mutanen e suka yi dafifi a wannan waje da wannan kamfani ya baje kolinsa. Masu kudi da wadanda basu da kudi kowa na samun abin da ya sawwaka daga wajen masu bayar da tallafin.