Kamfanin Gine-gine Na CITIC Ya Mika Sashen Karshe Na Aikin Ginin Babbar Hanyar Mota A Aljeriya
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kamfanin Gine-gine Na CITIC Ya Mika Sashen Karshe Na Aikin Ginin Babbar Hanyar Mota A Aljeriya

byCMG Hausa
2 years ago
CITIC

A jiya Asabar ne kamfanin gine gine na kasar Sin CITIC, ya mika sashen karshe na aikin ginin babbar hanyar mota da ta hade sassan larduna 17 dake kasar Aljeriya. Karkashin babban aikin ginin hanyar, CITIC ya kammala ginin kilomita 84 na hanyar.

Hanyar wadda ta hade sassan gabashi da yammacin kasar, ta dangana daga birnin Drean na lardin El Tarf a gabas mai nisa, zuwa birnin Raml Souk mai iyaka da kasar Tunisiya.

  • Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Gaggauta Gyara Kura-Kurai Da Bin Ka’idojin WTO

Yayin bikin kaddamar da sashen karshe na wannan katafaren aiki a birnin El Tarf, firaministan Aljeriya Aymen Benabderrahmane, ya jinjinawa muhimmin matsayin wannan aiki, wanda ya ce zai saukaka zirga zirgar matafiya, ta bunkasa hada hadar tattalin arziki tsakanin al’ummun Aljeriya da na Tunisiya.

Benabderrahmane, ya kuma yabi ingancin aikin hanyar, yana mai cewa, injiniyoyin kasar Aljeriya, da ‘yan kwadago da suka shiga aka dama da su a aikin, sun samu karin kwarewa da sanin makamar aiki.

Yayin bikin kaddamarwar, mataimakin babban manajan kamfanin CITIC a kasar Aljeriya Qi Shujie, ya ce injiniyoyin kasar Sin sun fuskanci manyan kalubale yayin da suke gudanar da aikin, ciki har da bukatar gudanar da ciko mai tarin yawa, da matsalar zaftarewar kasa, tun fara aikin ginin kilomita 84n a shekar 2017, amma duk da haka, sun kai ga kammala aikin a kan lokaci.

Kaza lika, wata sanarwa da kamfanin na CITIC ya fitar, ta ce kamfanin ya sauke nauyin dake wuyan sa, yayin da yake gudanar da ginin hanyar, wanda ya kunshi kafa cibiyar jagoranci, da ta lura da nagartar aiki, kana ya horas da dubban ma’aikatan hanya na kasar ta Aljeriya.

Har ila yau, kamfanin ya gudanar da ayyukan tallafawa al’ummun dake makwaftaka da aikin, ciki har da shiga ayyukan bunkasa jin dadin jama’a, kamar bayar da tallafi ga iyalai mabukata yayin azumin watan Ramadan, da gina filayen dakile yaduwar gobar daji, da samar da daukin ambaliyar ruwa. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
‘Yansanda Sun Cafke Wani Dan Tsibbu Da Kan Mutum A Jihar Ondo 

'Yansanda Sun Cafke Wani Dan Tsibbu Da Kan Mutum A Jihar Ondo 

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version