Connect with us

LABARAI

Kamfanin Infinix Ta Kaddamar Da Wayar ‘NOTE 5 Stylus’

Published

on

Kamfanin waya na Infinid ya bayyana  fitar da sabuwar waya, wadda ita ce ke jirin Ifinid wadda ake yayi yanzu, mai suna  Note 5 ta shiga kasuwa.

Bayanin daya fito daga kamfanin ya bayyana cewar  Infinid Note 5 an kera tane tare da hadin kan Google a matsayin Android 1 smart phone da kuma wasu abubuwan da duk ake sa ran za a gan su. Ita wayar kamar dai yadda kamfanin ya yi bayani, hakan yana daga cikin wasu abubuwan da yake son ya nuna wa su mutane cewar shi.

Ita wayar mum za ta samu tun daga ranar 10 ga watan Satumba, amma kuma daga baya sai   lokacin da za a  kawo ta  shagon sayarwa a ranar 17  ga watan Satumba.

“Mu a Infinid fatanmu shi ne mu samu ci gaba da bullo da wayoyio masu tafiya da zamani, da kuma yadda lokaci yake, wannan ma shi yasa shi yasa muka hada gwiwa da Google, cewar har yanzu dai bamu gaza ba sai gaba gaba, muka fito da Note5.

Da yake an fito da Note 5 Stylus yadda ta shigo kasuwa masu  sha’awar amfani da sabuwar dabara ta fasaha, kamar kamar yadda za a rikka daukar hoto mai kyau, da 16MP A1 rear camera, wadda take nuna fasaharsu, tare da Dpen mai kyau tare da taimakon Google Assistant, da kuma sauran wasu abubuwa mutum zai rika tattaunawa da duniya.” Shugaban Kamfanin Infinid Mobility Limited Benjamin Jian ya bayyana.

“Ko shakka babu muna tabbacin cewar yawar Note 5 Stylus zata samar wa  masu amfani da ita, kwanciyar hankali saboda za su samu biyan bukata, ba tare da bata lokaci ba.”

Kamar dai yadda kamfanin ya bayyana Note 5 Stylus an yi tane saboda ta kayatar da masu amfani da ita, data dai ta A1 camera masu daukar hoto mai kyau, har ila yau kuma ita wayar tana da wata kamarar da za a iya daukar hoto na selfie saboda tana da f2.0 aperture.

Saboda yadda aka kera ta fasahar zamani wadda ake ya yi, ita wayar ba zata bada kunya ba, wajen daukar hoto na selfie ko dai rana ko kuma dare.

Akwai ma wani abu da ake kira Dpen wanda shi ma wani abu ne, wanda ya samr da, sababbun dabaru da zasu taimaka ma masu amfani da wayar su bayyana kansu, da taimakon shi abin mai kama da Biro, masu amfani da wayar zasu iya yin gyara hotunan da suka dauka, ko kuma su rubuta wasu bayanai lokacin da ake taro.”

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: