Abdullahi Muhammad Sheka, , , , " />

Kamfanin KASCO Ya Samu Gata A Wajen Gwamna Ganduje – Kwamared Muhammad

Kamfanin samar da Takin Zamani tare da sauran kayan amfanin gona mai suna KASCO, Kamfanin ne da Jihar Kano karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, aka sakewa fasali tare da inganta shi wanda a halin yanzu ya zama zakaran Gwajin dafi wajen samar samar da taki a fadin wannan kasa baki daya.

Gwamna Ganduje ya yi dogon nazari tare da cire harkar siyasa daga cikin harkokin gudanarwa na wannan Kamfani inda gogaggen masanin siddabarun samar da kayan Noma da kuma sirrin kyautata dangantaka tsakanin manoma na kowanne fanni, Kwamare Bala Muhammad Inuwa ke jagoranta a matsayin  Manajan Daraktan Kamfanin na Kasco da ke Jihar Kano. Kamar yadda aka sani ne wannan Kamfani na da alaka ta kut da kut  da yunkurin Shugaban Kasa  Muhammadu Buhari na ganin an koma gona, saboda haka Gwamnatin Kano ta yiwa kamfanin garanbawul tare da damka Amanarsa a hannun wannan dan kishin kasa.

Babu shakka wannan kyakkyawan tunani na Shugaban kasa Muhammadu Buhari na wadata manoma da taki, Jihar Kano na cikin wadanda aka gayyata a lokacin da ake bukatar tsayar da farashin da ya kamata a sayar da takin zamani na bai daya domin Manoma su samu rangwame rahusa. Tarihi ya tabbata cewa Kamfanin na KASCO ya samu tsayawa da kafafunsa tun a shekarar 2016  wajen samar da taki tare da sayar da shi akan farashin Naira 5,500, saboda haka da wannan kuduri na Shugaban kasa ya shigo, sai aka zauna tare da kungiyar masu samar da takin zamani ta kasa da kuma sauran masu ruwa da tsaki a harkar noma domin samar da matsaya akan batun farashin da ya kamata a sayar da takin zamanin.

Bisa la’akari da kwarewar Kamfanin samar da Takin Zamani na Kano (KASCO) yasa wancan taron amincewa tare da tafiya bai daya da farashin Kamfanin na KASCO  ke  sayarwa akan kudi Naira 5,500, saboda haka sai kowa ya amince da a bar shi akan wannan farashi.  Kuma  duniya ta aminta da nagartar takin NA KASCO wanda hakan tasa ake rububin sayen sa daga ko’ina a cikin  Jihohin Kasar nan. Don haka Jihar Kano ta zama Zakaran gwajin dafi ta fuskar samar da takin zamani ga manoma, wannan kuma shi ne al’amarin da ke farantawa Shugaban kasa  Muhammadu Buhari rai na ganin an kama turbar hanyar dogaro da kai ta fuskar ciyar da kasa baki daya.

Wannan Kamfani na KASCO, mallakar Jihar Kano a koda yaushe na kokarin tabbatar da tsarin raba takin a kafatanin sito-sito da ke fadin Kananan Hukumomi 44 da ake da su. Kazalika,  kamar yadda Manajan Daraktan, Kwared Bala Muhammad Inuwa ya shaidawa Jaridar Leadership Ayau  cewa, yanzu haka jihohin Jigawa, Katsina, Kebbi har da ma wasu jihohin Kudancin kasar nan irin su Abakalike duk daga Jihar Kano suke sayen takin zamanin da manomansu ke amfani dashi a gonakansu.

Wasu daga cikin nasarorin da wannan Kamfani ya samu ya hada da samar da sinadarin yin takin zamanin wanda muke samu daga Katsina, haka nan bada jimawa ba bincike ya yi nisa na fara samun sinadarin a nan Jihar Kano kamar yadda Manajan Daraktan ya ambata. Haka zalika, tuni bincike ya tabbata cewa takin zamanin na KASCO yafi sauran duk wani taki da ake kawowa daga kasashen waje inganci, domin wanda ake kawowa jibge shi ake yi, sabanin na Kamfanin KASCO wanda ake samar dashi a lokacin da ake da bukatar sa kuma kowane iri muna da sirrrin yadda ake hada shi kuma ya zama ingantacce, Kamfanin ya samu wannan dama ne sakamakon gatan da Mai girma Khadimul Islam Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi masa ne sakamakon kishinsa a kan harkokin da shafi noma a wannan jihad a ma kasa baki daya.

Har ila yau, bisa la’akari da irin jajircewar Gwamna Ganduje a fuskar hakokin noma ya sa jama’a ke ganin kwalliya ta biya kudin sabulu tuni, domin da a ce maki za a baiwa Gwamnan a fannin noma, da sai a ce ya lashe jarrabawa 99%, sannan kuma wani abin ta’ajibi na wannan Kamfani shi ne yadda ya rike kansa da kansa, shike biyan albashi, kuma bashin da ya karba daga bangaren Gwamnati na Naira Miliyon 300 tuni ya biya Gwamnati har kuma da ribar Naira Miliyon 200, baya ga ci gaba da sayen manyan injunan aiki da kuma biyan duk wani hakkin ma’aikata.

Tsarin Kamfanin Takin zamani na KASCO na sahun gaba ta fuskar tallafawa ma’aikata aduk wani al’amari na rayuwa, haka muke bayar da tallafi alokutan azumi da sallah, idan lalura ta samu ma’aikacinmu muna bashi tallafi domin rage masa radadi, wannan tasa muke da kyakkyawar danganta tsaknin mu da abokan aikin mu. Haka kuma Kamfanin Kasco ba ya fukantar wata matsala ko ta gudanar da sarrafa taki, ko samar da kayan aiki,  Abinda kawai muke kara nema daga iyayen kasa da shugabannin kananan Hukumomin Jihar Kano 44 sun aminta da cewa kayan da muke kaiwa ma’ajiyar mu, su sani kayan sune kar bari wasu maras kishi su barnata su. Muna kuma fatan Jama’ar Karo zasu dubi wannan kyakkyawar aniya ta Gwamna Ganduje domin yaba kyauta da tukuici idan Allah ya kaimu kakar zabe mai zuwa. Inji Kwamared Bala Muhammad Inuwa Manajan Daraktan Kamfanin Kasco na Jihar Kano.

Exit mobile version