Kamfanin Kere-Keren Fasahar Aikin Noman Zamani Ya Tallafa Wa Manoman Karkara 60

RIFAN

Daga Abubakar Abba

A cikin bikin cikar Nijeriya shekaru 60 da kafuwa, wani kamfanin karfawa gwiwa manoman su sittin da ke a jihar Ogun.

An rarraba wadatattun kayan gona iri daban daban daga takin zamani, magungunan feshi, maganin rigakafi, abinci da yawa ga manoma.

Wannan shirin na karfafa gwiwa an yi shi ne da nufin taimaka wa manoma su bunkasa noman da dabbobin a gonakinsu daban-daban.

Da ya ke jawabi a shirin karfafa gwiwar, hadaddiyar kungiyar, Farmnow.ng, Samson Odegbami, ya bayyana cewa, an ba da tallafi ga manoman karkara ne daga larurar bayar da tallafi ga al’umma da kuma kara samar da abinci a cikin al’ummomin yankin don amfanin yankin.

Samson Odegbami yace, bayan bayar da taimako ga al’umma, na yi imanin yana da muhimmanci a matsayinmu na kungiya mu ba da gudummawa wajen magance matsalar karancin abinci ta hanyarmu.

A cewar Samson Odegbami, yunwa matsala ce mai matukar muhimmanci a kasar da ke bukatar a magance ta.

Samson Odegbami, ya ce ban da wannan, mun yi imanin karfafawa manoman karkara zai kara samar da abinci a cikin yankunansu da kuma ba su damar gudanar da aikin gona mai dorewa.

Samson Odegbami ya kara da cewa, an horar da manoman kan yadda za su ci gajiyar fasahar zamani domin bunkasa harkar noma.

Haka nan, a kokarinsu na cika burinsu na rarraba kayan amfanin gona da bayar da gudummawa ga wadataccen abinci na kasa, Farmnow.ng ta hanyoyi daban-daban na noma sun kirkiro da dandalin zuba saka gay an Nijeriya a ciki da wajen kasar.

A wani labarin kuwa, shugabanin kungiyar manoma ta kasa AFAN reshen yankin Kudu-maso-gabashin sun yi wasu yayan kungiyar dake gabatar da kanau a matsayin shugabannin kunkiyar da ke a shiyyar.

Shugaban kungiyar ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da suka fitar a yayin wani bayan babban taro na kwamitin kungiyar da aka gudanar a Enugu.

Shugabanin sune, na jihar Imo Dakata Bitus Ayo Enwerem; Mukaddashin Shugaban, reshen jihar Abia AFAN, Mike Obi Ekezie Shugaban kungiyar na reshen jihar Anambra Joe Madubuko; Shugaban ta na EnuguRomanus Eze; Mataimakin Sakatare na kasa, Princess Akunna Ubosi; Mataimakin Shugaban kasa na 1, Rabaran T A U Iwu.

Sauran su ne, Mataimakin shugaban kasa Cif Dan Okafor, Nnamdi Mekoh; Wakiliyar Mata ta kungiyar AFAN, dan IMO, Ambasada Ijeoma Nwachukwu; da Sakataren Yankin na AFAN, Comrade Sony Ekette.

Sanarwar an karanta tane bayan an tashi daga taron Kwamitin Yankuna na yayan kungiyar ta kasa wanda ya hada da dukkan Shuwagabannin Jihohi, sakatariyar jihohi, yayan kungiyar, Mata da Matasa matasa da kuma Jami’an kasa daga shiyyar da aka gudanar a Enugu.

Ban da jihar Ebonyi wanda har yanzu ba ta gudanar da zabubbuka na jihohi ba, dukkan sauran Jihohi suna da cikakken wakilci.

An yanke shawarwari masu zuwa ne a karshen taron, musamman na cewa, duk kungiyar Manoma ta kasa AFAN dake a yankin Kudu maso Gabas ta hana duk wani yunkuri da kowane daya daga cikin kungiyoyi ko da yaya aka fifita shi don krkirar kungiyoyi a cikin AFAN.

Exit mobile version