Kamfanin mai naOando ya samu zunzurutun riba ta Naira biliyan 4.6 bayan ya biya haraji a farkon wata shidan da suka gabata na shekarar bana. Kasuwar hannun jari ta Najeriya ce ta bayyana haka a wani rahoto da ta buga, haka kuma rahoton ya ci gaba da cewa, wannan babar nasara ce da Kamfanin ya samu, in an kwatanta da bara wanda ya yi hasara bayan cire haraji.
A wata takarda da kamfanin ya raba wa manema labarai ya nuna yadda kamfanin ya dawo aiki gadan-gadan a farkon wata shidan da suka wuce na shekarar bana, bayan fuskantar barazanar da suka yi daga tsagerun Neja-Delta.
Da yake karin haske kan yanayin gudanar da kasuwanci a yankin Neja-Delta, Shugaban kamfanin, Mista Wale Tinubu, cewa ya yi, saboda kwakkwaran matakin da gwamnati ta dauka ta fuskar tsaro a wannan yanki, yanzu haka tattalin arzikin Najeriya sai kara habaka yake yi, saboda ana samun walwalar gudanar da kasuwanci.Sannan sai ya kara dacewa, kamfanin ya samu nasarori masu yawa, a dukkan bangarorin da yake gudanar da harkokins kasuwancinsa.
A karshe Tinubu, ya ce, za su ci gaba da jajirce wa wajen tabbatar da kamfanin, ya samu nasarar da ake bukata, a kashi na biyu na karshen shekarar ta bana.