Connect with us

TATTALIN ARZIKI

Kamfanin Olam Ya Samar Da Shinkafa Tan 240,000

Published

on

Domin rage wa Nijeriya radadi bayan wucewar cutar Korona, kamfanin Olam Nigeria ya yi kokarin wajen bunkasa harkokin noma a cikin kasar nan. Ya bayyana cewa, ya samar da shinkafa wanda ya kai tan 240,000, a wani saban dubarin noma. Kamfani Olam Nigeria yana daya daga cikin kamfanonin noma a Nijeriya, ya bayyana cewa a halin yanzu tana ci gaba da noma filin noma wanda ya kai 5,000 hetta, wanda za iya noma tan 40,000 na shinkafa. Kamfanin yana da manoma a duk fadin wannan kasa, kamfanin ya samar da wannan ton na shinkafa ne a kauyukan Rukubi da Doma da suke cikin Jihar Nasarawa da kuma kauyen Amaraba Agro da ke cikin Jihar Kano, wanda ya samu tan shinkafa a wadannan kauyeka guda 120,000. A cikin bayanin kamfanin  Olam wanda ya gabatar da garin Abuja, ya bayyana cewa, yana kokarin samun hanyoyin da zai samu manoma  wanda suka kai 20,000, wanda za a ba su horo domin gudanar da noman shinkafa a cikin jihohi guda biyar da ke Nijeriya. Wannan zai gudana ne bisa umurnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci manoma su yi kokarin yin noma sasai, domin samun aminci saboda gwamnati ba ta da kudin da za ta shigo da abinci daga kasashen ketare a wannan shekara.

Bayanin ya gudana ne hakar haka, “manoma sun yi kokarin noma shinkafa tan 120,000 a kauyuka guda uku wadanda muka lissafa a baya, inda suka noma shinkafan da ake kira sa suna Mama Pride da kuma Mana Chioce.

“Bugu da kari, kamfanin Olam ya samu karin tan 100,000 a bangarorin Nijeriya ga manomanta da ke gudanar da harkokin noma a yankuna daban-daban da ke cikin kasar nan.

“Ya kamata mu manta da irin barnar da annobar cutar Korona ta janyo a yanzu na karyewar tattalin arziki. Lamarin bai tsaya a Nijeriya ba kadai ya shafi dukka tattalin arzikin Duniya ne.

“A kokarin da muke yin a tallafa wa Nijeriya wajen dakile barnar cutar Korona, kamfanin Olam ya samu nasarar tallafa wa a’lumma  cikin har da bai wa mata shinkafa da kayayyakin lafiya a cibiyar lafiya ta Rukubi da Doma da suke cikin Jihar Nasarawa da kuma gudanar wasu shirye-shirye na tallafi a mabambantan yankunan da ke cikin kasar nan. Haka kuma  kamfanin yana wayar da kai  a bangaren ilimi a rediyo da talabijin a haruka cikin gida a dai-dai lokacin da ake bukatar bayar da tazara a tsakanin mutane da saka takunkumi da kuma wanke hannu akai-akai, domin tabbatar da bin ka’idojin hukumar lafiya ta Duniya da hukumar da ke kuda da cututtuka a Nijeriya,” in ji Olam.

Kamfanin Olam yana da gonakin shinkafa da injin  nika a kauyen Rukubi da ke Jihar Nasarawa da kuma kauyen Amaraba Agro da ke cikin Jihar Kano, inda take da ma’aikata sama da 2,500 wanda ke taimaka wa mutanen karkara da ayyukan noma a yankunan da kewaye.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: