Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Kamfanin Olam Ya Shelanta Rage Kalubalen Rashin Wadataccen Abinci A Nijeriya

by
2 years ago
in NOMA
3 min read
Samar Da Abinci: Kamfanin Olam Zai Yi Hadaka Da Cibiyar Massachusetts
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Kamfanin na Olam a Nijeriya ya sanar da cewa, rungumar tsari na zamani zai taimaka wajen magance matsalar karancin abinci a Nijeriya.

Jami’in kamfanin na Olam a Nijeriya Mukul Mathur ne ya sanar da hakan ne a jihar Legas a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda kamfanin ya kara da cewa, ta hanyar hadar za su yi dukkan mai yuwa wajen rage matsalar samar karancin wadataccen abinci a kasar.

Ya ce, har yanzu muna fuskantar matsaloli kuma baza mu iya shawo kansu mu kadai ba, inda Jami’in kamfanin na Olam a Nijeriya Mukul Mathur, ya kara da cewa, mun fahimci kimar da mallakar tsari na zamani da zai taikama mana wajen shawo kan matsalolin, musamman ta hanyar samar da tsarin na zamani don a wadata Nijeriya da abinci.

Labarai Masu Nasaba

Kungiyar Noman Koko Za Ta Noma Tan 500,000 A Shekarar 2024

Sharhi: Rashin Karfafa Noman Auduga Tamkar Kamun Gafiyar Baidu Ne Ga Nijeriya

Jami’in kamfanin na Olam a Nijeriya Mukul Mathur ya ci gaba da cewa, yana da matukar mahimmanci a samar da wannan tsarin na zamani a tsakanin mutanen da ra’ayin mu yazo daya da nasu, inda ya kara da cewa, nayi amannar a tare, zamu iya shawo kan wadannan matsalolin dake a gaban mu.

An dai shirya taron ne don a janyo masu ruwa da tsaki dake a kasar nan domin su tattawa kan kalubalen da ake fuskatana a kasar nan na karancin wadataccen abinci, inda kuma suke son cimma wannan kudurin nasu a shekarra 2020.

Kamfanin Olam na kasa da kasa ya sanar da cewa zai yi hadaka da cibiyar fasaha ta Massachusetts don samar da tsarin da zai magance kalubalen da ake fuskanta wajen samar da wadataccen abinci a kasar nan.

Bugu da kari, taron an kuma gudanar dashi ne da nufin sada daidaikun jama’a da kamfani yadda zasu sanya ra’ayin su kan fanin kirkire-kire don a magance daukacin kalubalen rayuwa da da kuma na yanayi.

Jami’in kamfanin na Olam a Nijeriya Mukul Mathur an kuma ruwaito ya sanar da cewa, kamfanin na Olam, ya faro ne da mutum daya, kaya daya da ake sarrafawa a Nijeriya, inda kuma kamfanin na Olam, ya yin kokarin samun cimma manyan nasarori a cikin sama da shekaru 30.

Ita ma wata Jami’a a shirin MIT Sharon Bort, ta danganta shirin na MIT a matsayin daya daga matakan fita daga cikin kalubalen har a fadin duniya baki daya.

A cewar Jami’a ta shirin MIT Sharon Bort, shirin na MIT wanda aka fara a cikin watan Fabrairu, ako wacce shekara yana taimakawa wajen bude fagen yin gasa a fanonin tattalin arziki, daukaka, kiwon lafiya da kuma tabbatar da dorewa.

A karshe, Jami’ar ta shirin MIT Sharon Bort ta ce, an yanke shawara shirin na MIT zai mayar da hankali wajen magance daukacin kalubalen da ake fuskanta na karancin abinci.

A wata sabuwa kuwa, binciken ya nuna cewa, wasu kasuwannin dake a cikin jihar ta Katsina a satuttukan da suka gabata, ya nuna cewa, farashin sorghum mai nauyin kilohiram 100, ana sayar dashi kan kimanin naira 5,500, amma a yanzu, ana sayar dashi kan naira 7,500, kamar yadda wasu manoman jaridar Daily Trust ta tattauna dasu a jihar ta Katsina suka ce.

Daya daga cikin manoman Umar Audi ya sanar da cewa, aunngirgiza da sukaji cewar farashin sorghum ya tashi wanda a cewar su, a baya farashin bai tashi ba a wasu kasuwannin dake a cikin jihar ta Katsina ba.

ADVERTISEMENT

Ya yi nuni da cewa kamar yadda kake gani, an noma sorghum da yawa a jihar a shekarar data gabata domin mafi yawancin manoman jihar ta Katsina, a bara sun mayar da hankulan su ne wajen noman Shinkafa

Ya kara da cewa, hakannnenya sanya mu manomannda muka noma sorghum, muka yi tsammanin farashin zai tashi, amma abinda ya bamu mamaki shine yadda faraahinnya tashi daga naira 5,500 amma mun godewa Allah a yanzu farashin ya kai naira 7,500.

Ya danganta hakan kan garkame iyakokinnkanntudu na kasar nan da gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin ayi, inda ya sanar da cewa, saboda wannan matakin na gwamnatin.

Ya sanar da cewa, a yanzu, ana sayar da shinkafar gida a jihar kan naira 10,000 zuwa naira 11,000, inda ya yi nuni da cewa, ya danganta da irin kawun shinkafar ta gida.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Kasashen Afirka Za Su Iya Cimma Burinsu A Fannin Kere-keren Noma – Manaja

Next Post

Tsohon Sarkin Kano Ya Bayyana Hanyoyin Farfado Da Darajar Naira

Labarai Masu Nasaba

koko

Kungiyar Noman Koko Za Ta Noma Tan 500,000 A Shekarar 2024

by Abubakar Abba
3 days ago
0

...

Sharhi: Rashin Karfafa Noman Auduga Tamkar Kamun Gafiyar Baidu Ne Ga Nijeriya

Sharhi: Rashin Karfafa Noman Auduga Tamkar Kamun Gafiyar Baidu Ne Ga Nijeriya

by Abubakar Abba
2 weeks ago
0

...

Rogo

Noman Rogo: Yadda Nijeriya Ke Asarar Naira Tiriliyan 27 A Kasuwar Duniya

by Abubakar Abba
3 weeks ago
0

...

Gurjiya

Sirrin Noman Gurjiya Wajen Bunkasa Tattalin Arziki

by Abubakar Abba
1 month ago
0

...

Next Post
Nijeriya Na Iya Cigaba Da Zama Hedikwatar Talaucin Duniya –Sarkin Kano

Tsohon Sarkin Kano Ya Bayyana Hanyoyin Farfado Da Darajar Naira

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: