Rabiu Ali Indabawa" />

Kamfanin Sadarwa Ya Nemi CBN Kan Biyan Shi Tarar Dala Miliyan 285

Kamfanin sadarwar Interstella communication Ltd, ya yi kira ga babban bankin Nijeriya CBN da ya yi biyayya ga hukuncin kotun koli.

Tun a watan Disamba na shekarar 2017 aka yankewa babban bankin hukuncin tarar dalar Amurka miliyan 285 da zai biya kamfanin sadarwar wanda har a yau shiru kake ji. Kamfanin ya ce rashin biyayyar ga dokar kotun za ta iya jawo zubewar kimar kasar nan a idon duniya wani kamfanin sadarwa mai suna, Interstella communications Ltd, ya yi kira ga babban bankin Nijeriya CBN da su yi biyayya ga kotun koli ta hanyar biyansu tarar dalar Amurka miliyan 285 da aka yanke hukunci a sakamakon zarginsu da ka da karantsaye ga kwangila.

A ranar 15 ga watan Disamban 2017 ne kotun koli ta yanke wa babban bankin Nijeriyar hukuncin biyan tarar dala miliyan dari biyu da tamanin da biyar ga kamfanin sadarwa na Insterstella da Obi Thompson.

A yayin zantawa da manema labarai a ranar Litinin, Tony Nnadi, shugaban lauyoyin masu kara na shari’ar ya ce, an yi duk kokarin da ya dace wajen ganin babban bankin Nijeriya ya yi biyayya ga hukuncin amma ya ki. “Wannan abun zai iya jawo cece-kuce a duniya game da nagartar masana’antun kasarmu da kuma yadda suke daukar hukuncin kotu,” Nnadi ya ce. babban bankin Nijeriya CBN ya ki mai da martini ga wasiku uku da suka tura mashi. “A sakamakon hakan ne, wadanda suke bin babban bankin Nijeriyar bashi za su yi amfani da wata hanyar don tirsasa gwamnatin tarayyar biyayya ga dokar kotun kolin,” in ji lauyan.

An yi shari’ar ne sakamakon zargin cewa an karya yarjejeniyar kwangila tsakanin kamfanin sadarwar da babban bankin Nijeriya inda kamfanin sadarwar ya yi nasara.

Exit mobile version