Bello Hamza" />

Kamfanin Siminti Na Dangote Ya Samu Ribar Naira Biliyan 805. 6 A Shekarar 2017

Kamfanin Siminti na Dangote ya sanar da samun ribar Naira Biliyan 805.6 a karshen hada hadar shekarar 2017 (31 ga watan Disamba 2017).

Wadannan kudade ya ya nuna an samu karuwar kashi 31in a ka kwatanta da abin da aka samu na Naira Biliyan 615.1 a shekara 2016.

Hukumar hannun jari “Nigerian Stock Edchange (NSE)” ta bayar da wacan alkalummar, ta kuma nuna cewa ribar da aka samu kafin cire haraji ya karu da kashi 60.1 in aka kwatanta da Naira Biliyan 298.6 da kuma Naira Billion 180.9 da aka samu a shekarar 2016.

Haka kuma ribar da aka samu bayan cire haraji ya karu da kashi 43 zuwa Naira Biliyan 204.2 daga Naira Biiyan 142.9 da ka samu a shekarar 2016.

Kudaden ciniki ya kasance Naira Biliyan 351.3 maimakon Naira Biliyan 323.8 da aka samu a shekara 2016, ribar da aka samu gaba daya ya haura daga Naira Biliyan 454.3 maimakon naira Biliyan 291.3 da aka samu a shekarar da ta wuce.

Kudaden da aka kashi wajen aiyuka ya haura zuwa Naira Biliyan 125. 3 daga Naira Biliyan 119.3 yayin da kudaden harkkokin yau da kullum ya kai Naira Billion 16 maimakon Naira Biliyan 1.6 da aka samu a shekarar 2016.

Hukumar ta kuma aiyana Naira 10.50 a matsayin kudin kowanne hanun jari maimakon Naira 8.50 da aka biya a kan kowanne hannun jari a shekarar 2016.

Da ya ke sharhi a kan wadannan sakamakon, wani masani a FBNKuest ya ce, kudin hannunjarin ya yi dai dai da has ashen da suka yin a Naira 10.10 a kan kowanne hanun jari.

“Dama hukumar mu ta yi hashashen Naira 10.35 a matsayin hannun jari wanda hakan ya karu ne da kashi 24 lallai hakan ya yi daidai da has ashen mu na Naira 10.10 da Naira 10.70 da muka yi”.

 

Exit mobile version