Abubakar Abba" />

Kamfanin Simitin Dangote Ya Kaddamar Da Sabon Rahoto Da Rungumar Ka’idojin Kasuwar Sayar Da Hannun Jari

Kamfanin Siminti na Dangote wanda ya kasance shine kamfani a akan gaba da aka zayyana a kasuwara sayar da hannun jari ta kasa NSE ya fitar da rahoton san a shekarar  2018 da kuma nasarorin da kamfanin ya samu a cikin shekarar.

An kaddamar da rahoton na kamfanin Dangote ne a loakcin wani taro da kasuwar sayar da hannun jari ta kasa ta gudanar na ciyar da kasuwanci gaba da kuma samar da kyakyanwan yanayin yin kasuwanci, wanda ya yi daidai da ka’idojin kasuwar ta sayar da hannun jari.

A bisa gudanar da ayyukan ta a gurare uku a cikin kasar nan da kuma a cikin kasashe sha hudu dake a cikin nahiyar Afirka, kauswar sayar da hannun jari tana yin kokari wajen habaka tattalin arzikin da samar da kyakyawan yanayin day a dace don yin kasuwanci, har ila yau, wadannan hanyoyin sun hadada, bayar da rahoton koke na GRI.

A jawabin sa a lokacin taron Manajin Darakta na kamfanin Dangote Injiya Joseph Makoju,” Mun gano ana bin ka’ida da kuma gina aminta a inda muke gudanar da ayyukan mu.”

Babban Jami’I a kasuwar ta sayar da hannun jari NSE Mista Oscar N. Onyema, ya sanar da cewa, gabatar da rahoton ESG, zai taimaka wajen karfafa kasuar da kuma burin da ake dashi na habaka tattalin arzikin kasa.

Acewar Babban Jami’I a kasuwar ta sayar da hannun jari NSE Mista Oscar N. Onyema, an daidaita kasuwar ce don tayi daidai da tsari na duniya na yin kasuwanci kuma zamu ci gaba da zayyana daraja yin kasuwanci yadda hakan zai zamo alfanu ga kamfanonin da suka zuba jarin su a kasuwar don bayar da goyon baya wajen ciyar da tattalin arzikin kasar nan.

Exit mobile version