Daga CRI Hausa,
Kamfanin hada magunguna na Sinovac na kasar Sin ya sanya hannu kan yarjejeniya da kamfanin hada magunguna da samar da rigakafi na kasar Masar (VACSERA), domin kafa cibiyoyi masu sanyi don adana riga-kafi a Masar, ofishin jakadancin kasar Sin a Masar ya bayyana hakan a ranar Laraba.
Yarjejeniyar wanda kamfanonin kasashen biyu suka sanya hannu a wata ganawarsu ta kafar bidiyo da kuma a zahiri wanda ya samu halartar mai rikon mukamin ministan lafiya da ilmi mai zurfi na kasar Masar, Khaled Abdel-Ghaffar, da jakadan kasar Sin a Masar, Liao Liqiang, wanda aka gudanar a helkwatar ma’aikatar lafiya ta kasar Masar dake birnin Alkahira.
Ministan lafiyar ya bayyana a wajen bikin sanya hannun cewa, muhimmin matakin da kasar Sin ta dauka na samar da sabon rukunin alluran riga-kafin kimanin miliyan 10 ya kara bayyana kudurin kasashen Sin da Masar na yin hadin gwiwa da juna don yakar annobar.
Abdel-Ghaffar ya kara da cewa, Masar a shirye take ta cigaba da karfafa hadin gwiwa da kasar Sin don samar da riga-kafin a cikin gidan kasar, da yin masayar fasaha da yin bincike da bunkasa samar da magunguna, domin bayar da babbar gudunmawa wajen yaki da annobar a nahiyar Afrika. (Ahmad Fagam)