Kamfanin mai na Total Nigeria Plc yana tsammanin samun harajin da ya kai na naira biliyan 115.97 a farkon wata ukun shekarar 2021. Wannan tsammanin ya kai na kashi 157.7 kari da a kan na farkon wata ukun shekarar 2020, wanda ya samu. Wannan yana cikin bayanin ribar da kamfanin ya kai ke wa hukumar kula da kasuwan jari na Nijeriya.
Bayanan da manema labarai suka nada na mahimman rabar da kamfanin zai samu a farkon wata ukun shekarar 2021 ya nuna cewa, ana tsammanin samun karuwar riba wanda ya kai na naira biliyan 2.23 na kashi 55, yayin da yake tsammanin samun karuwar harkokin kasuwanci ta hanta ta musamman na naira biliyan 12.4 wanda ya kai na kashi 43.7.
Sauran kudaden shigan da kamfanin yake tsammanin samu sun hada da karuwar kudaden haraji na naira miliyan 811.8 wanda ya kai na kashi 117.7. yayin da yake tsammanin samun karuwar naira biliyan 2.6 wanda ya kai na kashi wajen saye da sayarwa. Kamfanin zai kashi naira 7.92 na kashi 31 wajen tsadar harkokin gudanarwa. Wanda yake tsammanin samun karuwarr ribar naira biliyan 2.7 na kashi 35. Daga karshe kudaden da yake tsammanin samu bayan ya biya haraji ya kai na naira miliyan 471 na kashi -16.1, wannan shi ne baban riba da kamfanin ke tsammanin samu a farkon wata ukun shekarar 2021. Kamfanin ya fitar da wannan tsammanin ne biya yadda masana suna lissafa farashin mai a shekarar 2021.