Idris Aliyu Daudawa" />

Kamfanin Total Ya Zuba Jarin Dala Biliyan 10 A Nijeriya

Kamfanin Total ya zuba jarin dala Bilyan goma saboda ya bunkasa sa hannun jari a Nijeriya, ta banagren mai da kuma iskar gas. Mista Ahmadu- Kida Musa, wanda shi ne mataimakin babban darekta na kamfanin Deepwater District, Total E and P Nigeria Ltd, shi ne ya bayyana hakan ne a, taron kungiyar ‘yan jarida masu aikawa da labaran da suka shafi wutar lantarki na kasa NAEC a Legas. Ya bayyana “ TOTAL manta wanda yake karkashin kasa yana taka muhimmiyar rawa, ta bangaren tattalin arziki da kuma ci gaban al’umma a Nijeriya saboda kuwa kashi goma sha biyar na man da ake hakowa a Nijeriya, Nijeriya ta kasance tana daga cikin abokan harkarmu, tana kuma da muhimmanci saboda tana samar da kasha 12 na a shekaru biyar da suka wuce.

A shekaru biyar da suka wuce kamfanin TOTAL ya zuba hannun jarin daya kai dala Bilyan10 a Nijeriya. “ Duk kuwa da yake da akwai matsaloli da suka muhallin da ake yin  shi al’amarin, kamfanin Total ya himmatu wajen sanya hannun jari a Nijeriya. Don  haka muke ganin idan Nijeriya ta samu ci gaba  shi ma kamfanin TOTAL ma ya samu “ Tutar Nijeriya tutar Nijeriya Mista Musa wanda shi ne ya bayyana muhimmancin dokar da ta shafi harkar mai, saboda ana iya yin amfani da shi, saboda a samu mafita daga matsalolin da ake fuskanta.

Ya kara jaddada cewa” Kamar dai yadda kuka riga kuka sani harkar man fetur dokar yadda ake tafiyar da ita, majalisun kasa suna amince da ita, cikin watan daya gabata, halin da ake ciki yanzu dokar tana jiran sa hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ita dokar data shafi bangaren man fetur ita ce ta farko a dokoki hudu wadanda suka shafi tafiyar da bangaren man fetur, wata doka da ta shafi shi bangaren man fetur wanda gwamnatin tarayya kawo ma shi bangaren gyara. “Sauran dokokin uku wadanda dukkansu suna ta shiga tsaren tsaren ‘yanmajalisu a majalisar kasa sun hada da Petroleum Industry  Administaratibe Billa (PIAB) Petroleum Industry Fiscal Bill (PITB) sai kuma Petroleum Host Community Bill (PHCB).

“Kamar dai abinda aka saba da shi wato yadda ake tunkarar wata sabuwar doka musamman ma wanda yake da muhimmanci kamar, dole ne tun farko a fara ganin alamun za a iya samun matsala. Amma kuma duk wadannan al’amuran da ake ganin su matsaloli ne, za a iya cimma maslaha ta hanyar lalama da kuma bangaren majalisa wajen sauraren ra’ayin jama’a. Damuwarmu da duk wani tunanin da zamu yi a kan PIGB abin ya ta’allaka ne a su dokokin wadanda abokan huldarmu ne na, masu samar da mai bangaren kasuwanci (OPTS) na kungiyar masana’antu da ‘yan kasuwa na jihar Legas.

Ya kara jaddada cewar su Shugabannin kamfanin TOTAL a Nijeriya da kuma masana’antar wutar lantarki, gaba daya suna alfahari da rawar da kake takawa, wajen samarc da daidaton kulawa da yadda al’amarain daya shafi banagaren wutar lantarki, abin ya zama akwai gaskiya da kuma da kuma rikon amana.

“Muna alfahari da yadda ‘yan kungiyarka suka maida hankali sosai da kuma irin yadda kuke bayar da rahotanni na hakikan dangane da wuraren da kuke ganin idan aka bisu za a cimma nasarori ta banagaren wutar lantarki.

Exit mobile version