Kamfanin Trust Ya Shirya Taron Manoma A Kebbi

Daga Umar Faruk, Birnin-Kebbi

Kamfanin Jaridar Daily Trust da hadin guiwar ma’aikatar Aikin Gona ta jihar Kebbi ta Shirya taron Manoma na kwana biyu a jihar Kebbi domin tattaunawa kan irin matsalolin da kuma irin abubuwa da yakamata kamfanin na Jaridar na Daily Trust yadace da ya taimakawa manoman jihar ta Kebbi kai.

Taron tattaunawar dai an gudanar da shine a daukin taro da ake bukin yaye Dalibai na kwalejen tarayya ta kimiya da fatasa da kuma kerekere wato Waziri Umaru Federal science and technology Polytechnic Birnin-Kebbi wato Shehu Kangiwa conbocation centre a jiya.

Da yake gabatar da jawabinsa shugaban kamfanin Jaridar Daily Trust kuma Edita in cif na kamfanin Alhaji Manir Dan – Ali ya bayyana cewa “kamfanin Jaridar Daily Trust ya Shirya wannan taron ne domin sanin abubuwa da ke damun manoma a jihar Kebbi da kuma fanin da yakamata kafafen watsa labarai su taimaka wurin ganin cewa sun gayawa duniya irin kokari da kuma Kwazon da manoman jihar Kebbi keyi ta hanyar taimakawa gwamnatocin jihar da kuma tarayya domin bunkasa tattalin arzikin noma a jihar Kebbi da kuma kasar nan bakin daya.” Wanda yin hakan ga manoman jihar ta Kebbi ya taimaka ainun ga dawowa da tattalin arzikin noma a kasar nan.

Hakazalika yace saboda irin Kwazon da Manoman jihar keyi shine yasa kamfanin Jaridar Daily Trust keson tattaunawa da mano a jihar domin tallafa musu ta hanyar watsa Kwazon da su keyi ga duniya.

Daga karshe ya yi kira ga manoman na jihar ta Kebbi da su maida hankalinsu ga abubuwa da za’a tattaunawa a wurin taron na kwana biyu. Ya kuma godewa gwamnatin jihar Kebbi da kuma ta tarayya kan irin goyon bayan da ake baiwa kamfanin Jaridar Daily Trust a kasar nan bakin daya.

Shi ma a nashi jawabi Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu bayyana cewa kafafen watsa labarai na da muhimmiyar rawar da su iya takawa wurin yada abubuwa da Manoma keyi a jihar Kebbi da ma wasu jahohin kasar nan dake Aikin noma.

Har ilayau Gwamnan yace “dukkan ci gaban da aka samu a jihar ta Kebbi kan harakar noma ta taimakon ‘yan jarida aka sameshi”. Yace samar da shinkafar LAKE RICE a kasar nan na cikin nasarorin da noma ya samu a kasar nan a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari. Hakazalika ya gwamnatin tarayya ta amince da ta kara saka jarin Naira biliyan day na dalar Amurka ga harakar noma a kasar nan wanda za’a samu riba fiye da man fetur.

Daga nan yayi kira Manoma, sauran gwamnatocin jahohin kasar nan da kuma masu ruwa da tsaki na kasar nan da su ci gaba da bada goyon baya ga harakar noma a kasar nan domin rage dogaro ga man fetur.

Manyan bakin da suka halarci taron da kamfanin Jaridar Daily Trust ta Shirya sun hada da mistan Aikin Gona Audu Ogbeh wanda Inginiya Abdullahi Shehu ya wakike, Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu, Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi kanar Mai ritaya Samaila Yombe Dabai, Mai Martaba Sarkin Gwandu janar mai ritaya Muhammadu Iliyasu Bashar, Mai tsawatarwa a majalisar dattijai Sanata Adeyeye, Kwamishinan Gona na jihar Kebbi Alhaji Muhammad Garba Dandiga, Shugaban kamfanin NNPC Inginiya Maikanti Baru wanda Alhaji AbdulGaniyu ya wakilta da shuwagabannin bakunan Manoma a kasar nan da kuma wasu hukumomin kula da harakar noma a kasar nan da sauran.

Exit mobile version