Connect with us

LABARAI

Kamfanin Volkswagen Zai Fara Hada Motoci A Nijeriya

Published

on

Gwamnatin tarayya  da hadin gwiwar kamfanin kera motoci na Bolkswagen sun kulla yarjejeniyar fara harhada motoci a Nijeriya.

A karkashin wannan yarjejeniyar kamfanin Bolkswagen zai samar da wani tsari na sharar fage a kan harhada motoci wanda kuma daga nan ne ake fatan  Nijeriya za ta fara kera motoci  wadanda za a yi amfani da su a cikin kasa da kuma wasu kasashen Afirka.

Ministan masana’antu da kasuwanci da zuba jari Dakta Okechukwu Enelamah, ne ya sa hannau a yarjejeniyar a madadain gwamnatin tarayya daga kuma bangaren kamfanin na Bolkswagen, shugaban kamfani yankin Afirka Thomas Schaefer, ne ya sa hannau.

Yarjeniyar za ta ba kaungiyar dama kafa Cibiyar horaswa da hadin gwiwar gwamnatin kasar Jamani domin samar da ayyukan yi.

Daga cikin ayyukan Cibiyar da zaa kafa akwai bayar da horo a kan gyaran mota.

Za kuma ta samar da motoci masu yawa kirar Bolkswagen a cikin gida Nijeriya domin amfanin ‘yan kasa da kuma wasu kasashen da za su kulla yarjejeniyar kasuwanci da su.

Enelamah  ya fada lokcin kulla yarjejeniyar cewa babban ci gaba ne wajen samar da motoci.Wannan wani abu ne da zai kara bunkasa tattalin arzikin wannan kasa ta Nijeriya.

Ya ce, mun tabbatar da cewa wannan wata hanya ce da za ta taimaka wa Nijeriya wajen bunkasar tattalin arzikinta musamman ta fuskar samar da sifuri, haka kuma sun yi alkawarin yin aiki tukuru na ganin cewa wannan manufa ta samu cikakkiyar nasara, musamman yadda wadanda suka zuba jari za su ci moriyar abin da suka zuba.

”A shirye muke  mu yi aiki da wadanda suke aiki a wannan kamfani a baya, yadda za mu kara samun karfin gwiwar ci gaba  wannan aiki da muka sa a gaba yadda za mu wadata gida da samar da wadanda za a sayar a kasashen waje.”

Shi ma da yake na sa jawabin babba daraktan kamfanin harhada motoci, Jelani Aliyu, ya ce kasanacewar  Nijeriya cibiyar kasuwanci za ta amfana ta wannan kasuwanci a cikin gida sannana kuma zai zamar mata mabudi na huldar kasuwanci da wasu kasashen yammacin Afirka.

Ya ce, “Ya zuwa yanzu mun gamsu bisa yarjejeniyar da muka kulla da kamfanin Bolkswagen, kuma ya kara mana karfin gwiwa da nkuma kara zakulo ma’adanan da muke da su tare da sarrafa su a wannan kasa.”

Haka kuma Schaefer  ya ce kulla wannan  yarjejeniya ya nuna azamar da wannann kamfani yake da ita na bunkasa harkokin kasuwanci a kasashen yammacin Afirka.

“Za mu ci gaba da kokarin ganin mun bunkasa harkokinmu a kasashen Afirka tare da bunkasa tattalin arzikin yankin ta fuskar kera motoci.”

Advertisement

labarai