Kamfanina Na Rage Wa Gwamnati Nauyin Samar Wa Matasa Aiki A Kano – Sani Tsoho

Aiki

Daga Bala Kukkuru,

Wani sanannan dan kishin kasa da ke zaune a jihar kano kuma shugaban kamfanin ‘Cican Engineering’ dake hada injunan gyaran kayan amfanin gona a jihar kano da kasar nan baki daya mai suna Alhaji sani tsoho da ke unguwar masaka gwambaja a cikin birnin kano, ya yi tsokaci a bisa yadda da yake ganin kamfaninsa na ragewa Gwamnatin Nijeriya nauyin samarwa matasa aikinyi a jihar kano da kasar baki daya.

Shugaban ya yi wannan tsokaci ne a garin kano a yayin da yake zantawa wakilan kafofin yada labarai na kasa, wadanda suka hada da wakilin mu na ‘Jaridar Leadership A Yau’ na jihar Legas, lokacin da ya halarci taron jajantawa manoman a rewacin Nijeriya wanda kwamitin kasuwar ‘mile12 Intanashinal market’ ta gudanar a cikin jihar kano, a makon da ya gabata inda Shugaban kamfanin na ‘Cican Engineering’ ya halarta.

Alhaji sani tsoho ya ci gaba da cewa, babu shakka wannan kamfanin na shi yana daya daga cikin kamfanonin da ke tallafawa Gwamnatin jihar kano da ta kasar nan baki daya ta bangaren samarwa matasa aikinyi da al’ummar cikin kasar nan gaba daya, idan aka yi la’akari da irin yawan matasa da sauran al’ummar da suke cin abinci a cikin kamfanin suna da yawan gaske, a cewar al’amarin da ya kawowa Gwamnatin jihar kano saukin radadin samarwa matasa aikinyi a jihar dama sauran wasu sassan jihohin kasar nan.

Ya kara da cewa, a kan haka yake shawartar sauran masu kudin jihohin kasar nan da su cigaba da bude irin wadannan matsakaitun masa’antu domin ciyar da kasar nan, tare da ragewa Gwamnati saukin jin radadin samarwa matasa da sauran al’umma aikin yi a kasar baki daya.

Sannan ya ci gaba da ba Gwamnati shawarwari a game da yadda za ta samu guraben samarwa matasa da sauran al’umma aikin yi a kasar, in ji shi, kamar yadda ya ga kasar Sin yake yi wajen samarwa matasa da aikin yi da samar da wani abu da bangaren yake amfani dashi.

Ya ce, da fatan Nijeriya zata yi amfani da wadannan shawarwari. Sannan kuma ya cigaba da yaba wa Gwamnatin Nijeriya a bisa ga kokarin da take yi a wajen dakile annobar cutar korona a duk fadin kasar, wanda bayyana da cewa, babu shakka kasar tana cigaba da kokari a wajen shawo kan wannan annobar, domin ita ta sanya wasu kasashen duniya suka rasa rayuwar dumbin al’ummarsu, amma Nijeriya Allah ya taimake ta ba ta rasa irin wannan adadin rayukan ba, da fatan Allah uban giji ya cigaban da kare al’ummar musulmin Nijeriya da duniya baki daya.

 

Exit mobile version