Kamfanin mai na kasa (NNPC) ya bayyana cewa, akalla kamfanoni guda 96 suke takarar samun kwangilar gyara bututun man Nijeriya. kamfanin NNPC ya bayyana cewa, za a bayar da kwangilar bututun mai ga kamfanoni masu zaman kansu domin a can za su zuwa na zama. A cewar kamfanin, bayar da kwangilar yana bisa tsarin kokarin NNPC domin tabbatar da kyakkywan shugabanci.
Da yake jawabi a wurin taron, shugaban kamfanin ‘Nigerian Pipelines and Storage Company (NPSC)’, Ada Oyetunde ta bayyana cewa, gwamnati tarayya ta dauki matakin gyara bututun mai a fadin kasar naan. Oyetunde ta bayyana cewa, gwamnatin tarayya za ta gyara bututun mai da ke rarraba danyan mai ga matatun mai a cikin kasar nan tun daga tashoshin mai na wajen sari har zuwa defot. Ta kara da cewa, za a gudanar da wannan aiki saboda zai taimaka wa matatun mai wajen kai man a ko’ina bayan an kammala.
“Bisa haka ne ya sa gwamnati ta bude kofa ga kamfanoni masu zaman kansu wadanda suke sha’awar wannan kwangila tun a watan Agustaan shekarar 2020, bututun man wanda ya hade matatun mai kamar matatan mai na Fatakwal da matatan main a Warri da matatan mai na Kaduna,” in ji Oyetunde.
Ta ci gaba da cewa, samar da kyakkyawan bututun mai zai taimaka wajen ijiye danyan mai ga matatun mai da ke kasar nan. Ta ce, zai bayar da samun daman saka farashi da kuma zuwa ba jari da karin kudin mai da aka yi a baya.