Yusuf Shuaibu">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home TATTALIN ARZIKI

Kamfanonin Jiragen Sama 18 Sun Kasafta Naira Biliyan Hudu Na Tallafi

by Yusuf Shuaibu
January 5, 2021
in TATTALIN ARZIKI
2 min read
Kamfanonin Jiragen Sama 18 Sun Kasafta Naira Biliyan Hudu Na Tallafi
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Gwamnatin tarayya ta bai wa kamfanonin jiragen sama guda 18 da ke cikin gida Nijeriya naira biliyan hudu, a matsayin kudaden tallafi.

An bayyana cewa, an kasafta kudaden ne bisa yanayin gudanar da harkokin jigila. An bai wa kamfanonin jiragen sama wadannan kudade ne a matsayin tallafi ga cutar Korona. Kamfanonin sun sami wadannan kudade sakamakon irin asarar da suka tafka lokacin dokar hana zirga-zirga wanda gwamnati ta kafa saboda cutar Korona.
Da yake kare kasafin kudin shekarar 2021 na ma’aikatar sufurin jiragen sama a gaban ‘yan majalisa, minista Hadi Sirika ya bayyana cewa, an ware naira biliyan biyar ga bai wa kamfanonin jiragen sama tallafi.
An bayyana cewa, kamfanin jiragen sama sun fuskanci matsaloli masu yawa lokacin cutar Korona, wannan ne dalilin da ya sa gwamnati ta samar musu da kudade na musamman domin farfadowa daga matsalolinsu. A baya dai, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya rarraba wa kamfanonin naira biliyan 27 a karkashin shirin farfado da tattalin arziki.
Wata majiya daga ma’aikatan jirage saman ta tabbatar da bayar da kudaden, ta ce ta bai wa kamfanonin ne bisa alkawarin da ta yi musa a baya na ba su biliyan biyar, amma a yanzu an fara ba su biliyan hudu saura biliyan daya.
Da yake mayar da martani, shugaban kamfanin Skypower Edpress Airways, Kaptain Mohammed Joji ya gode wa gwamnatin tarayya bisa bai wa kamfanonin tallafin kudade. Ya bayyana cewa, kamfanonin jiragen sama sun fuskanci matsalolin kudade wanda takai har ma wasu daga cikin su ba sa iya biyan albashi ga ma’aikatansu, yayin da wasu kuma koyar ma’aikatan suka yi daga aiki.
“Muna matukar nuna godiyarmu da wannan tallafi. Minista da shugaban hukumar kula da filayen jiragen sama sun yi matukar yi mana kokari,” in ji shi.
Ya kara da cewa, wasu daga cikin wadanda suka sami wannan tallafi zai taimaka musu wajen farfadowa daga matsalolin da suka fuskanta lokacin dokar hana zirga-zirga. Ya ce, daga cikin kamfanonin an samu asarar kudade wadanda suka kai tsakanin naira biliyan 360 zuwa naira biliyan 500.
An dai fuskanci dokar hana zirga- zirga na tsawon wata uku wanda ya janyo hana sama da kamfanoni 120 gudanar da harkokin kasuwanci, amma a yanzu kamfanonin jiragen saman suna kokarin farfadowa daga matsalolin lamarin.
Kamfanoni 18 ne suka mika bukatarsu na neman kudaden tallafin cutar Korona. A cikin su akwai manya-manyan kamfanoni wadanda suka hada da Dana Air da Mad Air da kuma Azman Air.

samndaads
SendShareTweetShare
Previous Post

Takwaran Hitler Ya Lashe Zabe A Kasar Namibiya

Next Post

An Rasa Naira Biliyan 645.15 A Bangaren Lantarki A 2020

RelatedPosts

Kangin Talauci

Shirin Tsamo Mutane Miliyan Biyu Daga Kangin Talauci Ya Kankama – Osinbajo

by Yusuf Shuaibu
3 days ago
0

Bayan samun nasarar kaddamar da shirin farfado da tattalin arziki...

Talakawan Nijeriya

Talakawan Nijeriya Miliyan 24.3 Sun Samu Tallafin Naira 5,000 Kowanne – Ministar Jinkai

by Yusuf Shuaibu
3 days ago
0

A ranar Talata ne, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, sama...

FIRS

FIRS Ta Tattara Harajin Tiriliyan N4.9 A Shekarar 2020 Duk Da Korona

by Yusuf Shuaibu
4 days ago
0

Hukumar tattara haraji ta kasa (FIRS) ta bayyana cewa, ta...

Next Post
Rashin Wutar Lantarki

An Rasa Naira Biliyan 645.15 A Bangaren Lantarki A 2020

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version