Kamfanonin da ke rarraba wutar lantarki a Nijeriya sun yi barazanar dakatar da aiki matuƙar Gwamnatin Tarayya ta gaza biyan su bashin da ya kai Naira Tiriliyan huɗu da suke bi.
Shugaban ƙungiyar kamfanonin, Kanal Sani Bello, ya fitar da sanarwa yana cewa rashin wannan kuɗi yana jefa su cikin mawuyacin hali, inda ya ce ya zama dole su ɗauki wannan mataki domin tilasta wa gwamnati ta biya su haƙƙoƙinsu.
- Za A Watsa Shirin Bidiyon “Bayanan Magabata Dake Jan Hankalin Xi Jinping” Na Harshen Malay
- Gazawar Gwamnati Kan Kiyaye Rayuka Da Dukiyoyi: Gwamnan Filato Ya Nemi Yafiyar Al’ummar Jihar
Barazanar yajin aikin na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ke shirin haramta shigo da farantan adana hasken rana (solar panels) daga ƙasashen waje, wanda ya jefa damuwa a zukatan al’umma da ke fargabar ƙara samun matsalar wuta.
Kamfanonin sun bayyana cewa hauhawar farashin dala da harajin da ake ɗora musu su ma sun ƙara dagula lamarin, yayin da su kuma suka fuskanci tara daga gwamnati saboda tuhumar su da aringizon kuɗin lantarki.
Idan gwamnati ba ta ɗauki mataki ba cikin gaggawa, akwai yiwuwar a sake shiga duhu a sassa daban-daban na ƙasar nan.