Mustapha Ibrahim" />

Kamfanonin Shinkafa Na Yunkurin Canja Manufar Buhari Ta Rufe Iyakar Kasa – Hamir

Guda daga cikin fitattun Matasan ‘yan kasuwa na Jihar Kano, Alhaji Rabiu Hamisu Hamir ya bayyana cewa, rufe iyakokin kasar nan da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi, ya aiwatar da shi ne da kyakkyawar niyya ta yadda Nijeriya za ta mu nasarar dogaro da kanta tare da tsayawa da kafafuwanta ta fuskar noman shinkafa da sauran abubuwa da za su taimakawa kasar nan ta kowane irin fanni, musamman idan aka yi la’akari da manufar Shugaban a kan harkokin noman da sauran ayyukan raya kasa.

Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, yadda masu kamfanonin shinfaka suke amfani da wannan dama wajen cin karensu babu babbaka, ta hanyar kara wa shinkafar farashi a kullum ta Allah, ga kuma rashin wadatar da mabukata shinkafar a kasuwanni, wanda wannan kamar wani abu ne da masu kamfanonin shinkafar ke yi da nufin canza manufar Shugaban kasa ta rufe iyakokin dmin amfanin kasa. Babu shakka, wadannan kamfanonin sarrafa shinkafa na yunkurin jefa al’umma cikin karancin shinkafar da kuma tsauwala wa mabukata farashi fiye da kima da kuma jefa su cikin halin kaka-na-ka-yi, wanda ba ita ce manufar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba, kamar yadda ni na fahimta, a cewar Hamir.

Matashin Dan kasuwan ya kara da cewa, hakika akwai dan kasuwa a kusa ba a nesa ba, wanda a kullu-yaumin yana sayar da akalla Tirela biyar, wato huhu 3,000 a kowace rana, amma ga yanzu shi ma ko Tirela daya baya iya samu a rana. Don haka, ina ne yanzu mutane za su iya zuwa su samo wannan shinkafa, tunda da dai duk kasuwar Singa da ke Kano, ba za ka iya samun Tirela daya ta shinkafa ba, wacce kuma ita c eta zama abincin yau da kullum ga galibin mutanen Nijeriya a wannan lokaci, in ji shi.

Haka zalika, Alhaji Hamir ya yi kira tare da bayar da shawara ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, akan ya sa ido tare da kawo kyakkyawan tsari akan wadannan kamfanoni na shinkafa, ta yadda za su fito da shinkafar cikin sauki domin jama’ar Nijeriya su samu cin gajiyar wannan manufa ta Muhammadu Buhari, da kuma samun wadataccen tsaro a tsakanin al’ummar Nijeriya bakidaya.

Amma yanzu yadda wadannan kamfanonin shinkafa ke boye ta tare da sake kara mata farashi, kai tsaye wannan na nuna alamu da ka iya jefa al’ummar wannan kasa cikin matsala ta karancin abinci da gan-gan. Don haka, wajibi ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya san wannan matsala tare da kokarin gaggawar daukar mataki a aikace, domin ceto al’ummar Nijeriya daga karancin abinci sakamakon tarnaki da kokarin zagon kasa ga manufar Shugaba Buhari. Sai dai kuma duk wani kokari da Leadership A Yau ta yi don jin ta bakin wadannan masu kamfanonin shinkafa dangane da wannan zargi da ake yi musu a Kano, abin ya ci tura.

Exit mobile version