Kamfanonin Siminti Sun Koma Yin Hanyoyin Kankare A Nijeriya

Daga Sabo Ahmad

A halin yanzu kamfanonin yin siminti na Nijeriya, sun koma yin hanyoyin kankare a wasu bangarori na kasar nan, don koma wa da kasar cikin sahun kasashen duniya da ke amfani da fasar yin kankare wajen yin hanyoyi wanda ke bayar da gudummowar samun ci gaban tattalin arzikin kasa da bunkas rayuwaral’umma. Yanzu haka a duniya akwai kasashe 50 da ke amfani da fasahar kankare ta, “Roller Compacted Concrete” (RCC) da “Traditional Concrete” da “Thin Concrete Pabement” (TCP), wajen aikace-aikacen hanyoyi. A kasashen Afirka kuwa, kasar  Afirka ta kudu da Kenya da Masar da Gana ne kadai ke amfani da sabuwar  fasahar, wajen yin hanyoyinsu.

Femi Yusuff, shugaba mai kula da sahin hanyoyi na kamfanin Lafarge Africa Plc, ne ya bayyana hakan lokacin da yake zanta wa da ‘yan jarida a garin Legas. Ya ci ga ba da cewa,” Yadda kamfanin siminti na Lafarge da Dangote da BUA ke samar da tan miliyan 40 na siminta ya isa a yi amfa da shi, wajen yin duk wani aikin kankare a kasar nan”

Ha kuma ya ce, “kamfanin siminti na Lafarge, ya fara yin hanya ta kankare a wadasu manyan birane guda uku da ke Nijeriya watau: Kalaba da Oshogbo da Gombe. “Muna aikin hanya mai tsawon kilomita 7.5 daga Lafarge zuwa Unicem Ebacuation, da ke Kalaba a kan naira miliyan 700, sai aikin kilmita 8 a Maiganga, jihar Gombe wadda kamfain Ashaka ya yi sai kuma ta Oban road wadda ta hada Kalaba da kasar Kamaru sai kuma ta Oshogbo da ke  jihar Osun”.

Femi ya ci gaba da cewa, titin kwalta na da kyau a fuska amm sai dai ba ya dade wa kamar yadda na kankare ke dade wa. Ya ce, duk da tsadar aikin kankare in aka kwatanta da kwalta za a ga akwai sauki domin yana dade wa bai lalace ba, sannan kuma yana da sauki wajen kula da shi. A halin yanzu kamfanin siminti na Dangote ya yi hanyar Apapa da ke garin Legas da kuma hanyar wani kamfanin simintinsu da ke garin Ibeshe a jihar Ogun, wanda ke nuna irin nasara da ka samu ta wajen yin amfani da wannan sabuwar fasa.

Exit mobile version