Kamfanin Hisense South Africa, da kamfanin CNBM, sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa bisa matsayin koli, ta gudanar da aikin samar da hidimomin kyautata amfani da makamashi mai tsafta a Afirka ta kudu.
Kamfanonin biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a jiya Talata, a birnin Johannesburg, yayin bikin baje hajojin da suka shafi sabbin makamashi, daya daga baje koli mafi girma da ake gudanarwa a nahiyar Afirka a fannin makamashi mai tsafta, wanda ke gudana yanzu haka a birnin.
Bayan sanya hannu kan yarjejeniyar, babbar manajan sashen lura da hadin gwiwar kamfanin CNBM a kasashen ketare Jiang Fei, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua cewa, sabon hadin gwiwar zai taimakawa Afirka ta kudu, da ikon cin gajiyar isasshen makamashi.
Jiang Fei ta kara da cewa, kamfanin Hisense South Africa da CNBM, za su samarwa ‘yan kasar mitoci irin na zamani, da wuraren caji, da ma’ajiyar makamashi da sauran hidimomi na zamani, wadanda za su baiwa Afirka ta kudu damar sauya alaka zuwa amfani da makamashi mai tsafta. (Mai fassara: Saminu Alhassan)