Kammu A Hake Yake Wajen Ciyar Da Kasuwar Mile 12 Gabas

Sabon shugaban kungiyar masu sayar da busashen barkono a babbar kasuwar sayar da kayan gwari dake unguwar Mile 12, Alhaji Muktar Jabo kan asalin jihar Jigawa wanda yake gudanar da harkokin sana’arsa ta busashen barkono a Mile 12 ya bayyana cewar shida sauran shugabannin bangare daban daban na kasuwar Mile 12 kansu a hake yake a wajen ciyar da kasuwar gaba.

Sabon shugaban bangare kasuwancin busasshen barkono ya yi wannan furuci ne a offishin kungiyar jim kakan bayan da kwamitin kasuwar ta Mile 12 ta kaddamar dasu a matsayin sababbin shugabannin bangarorin kasuwar wakanda za su ci gaba da kare mutuncin kasuwar kafin nan da wakansu shekaru masu zuwa, Alhaji Muktar Jabo ya ce, wajibi ne sababbin shugabannin bangarorin kasuwar ta Mile 12 su cigaba da haka kawunan junansu domin neman karin zaman lafiya sannan kuma su dukufa a wajen nemo hanyoyin da za su ciyar da kasuwar gaba taron kaddamar da sababbin shugabannin kasuwar wanda ya gudana a ranar Alhamis data wuce shugabannin da kwamitin kasuwar ya kaddamar da bangaren kasuwancin busashen barkonon sun haka da shi kansa Alhaji Muktar Jabo a matsayin shugaban bangaren busashen barkono da mataimakinsa Alhaji Usaini Madobi da Sakataren kungiyar gaba kaya Yunusa Isiyaku Madobi mataimakinsa Lukuman Bayarabe  da ma’ajin  kungiyar Alhaji Bala Ruma da mataimakinsa Alhaji Gali Madobi sai Sakataren kuki Alhaji Umaru Madobi da mataimakinsa Yusif Mohmed Jos sai kuma Mai binciken Kukin kungiyar Alhaji Sule Bita Madobi sauran sun haka da Alkalin kungiyar, Alhaji Saminu Magaji na Sani Zarewa da sauran makamantansu.

A jawabinsa kuma da hukuba ga sababbin shugabannin bangarorin kasuwar, shugaban kasuwar Alhaji Shehu Usman Sampam ya ummurcesu da cewa kowannansu ya zama jakada nagari a wajen bangaren sana’arsa da kuma nemo hanyoyin da za su ciyar da bangaren su gaba da kasuwar ta Mile 12 baki kaya a ci gaba da bayaninsa, sabon shugaban Alhaji Muktar Jabo ya nuna farin cikinsa ne game da wannan matsayi da Allah ya sake bashi na shugabancin kasuwar suka tabbatar masa dashi yana mai godiya a garesu da fatan  Allah ya bar  zumunci sannan kuma ya ci gaba da isar da sakonsa na godiya ga dattawan  kasuwar kamar su Alhaji Isa Mohmed da Alhaji Habu Paki da Alhaji Haruna Tsohon Shugaban kasuwar da Alhaji Abdul Wahab Tsoho Babangida da sauran jama’ar da suka haka shawarwari a wajen sake bashi wannan mukami a ya kuma yi fatan Allah ya saka masu da alhari, ya kara da cewa, suma za su yi iyakar kokarinsu a wajen gudanar da mulkin bangarorin a cikin adalci kamar yadda  sauran shugabannin suka yi domin samun ci gaban kasuwanci da kuma zaman lafiya baki kaya.

Sauran jawaban sababbin shugabannin da sauran jama’a a wajen taron kaddamarwan sun karkata ne a wajen shugaban kasuwar Alhaji Shehu  Usman  Sampam a kokarinsa na ciyar da kasuwar da sauran al’ummar cikinta gaba baki kaya.

Exit mobile version