Umar A Hunkuyi" />

Kan-iyakokin Nijeriya Za Su Ci Gaba Da Kasancewa A Garkame – Hamid Ali

Shugaban hukumar yaki da fasa-kwauri ta kasa, Hamid Ali, ya bayyana cewa kan iyakokin Nijeriya za su ci gaba da kasancewa garkame har sai lokacin da kasashen da ke makwabtaka da Nijeriya suka dena bai wa masu fasa-kwauri shigo da kayan da kasar sa ta haramta shigowa dasu.

Shugaban hukumar ya yi wannan furucin ne a tsakiyar mako a sa’ilin da ya ziyararci Maigatari, da ke jihar Jigawa; wanda yake kan iyakar Nijeriya da jamhuriyar Nijar. Ya ce Nijeriya ba za ta taba yin shiru da zuba ido ta kyale wadannan kasashen su kassara tattalin arzikin ta ba. Ali ya shaida wa yan jarida cewa wadannan kasashen da suka hada makwabtaka da Nijeriya sune kanwa uwar gami wajen mara wa  masu safarar iri-iren wadannan kaya da suka haramta shigo dasu tare da cewa kuma kasashen sun san yadda fasa-kwaurin irin wadannan kayayyakin zai yi ga ci gaban Nijeriya. Ya ce duk da yadda suka dauki kwararan matakai, amma kuma kofar tattauna a kan lamarin a bude take wajen samun fahimtar juna da sabuwar yarjejeniyar da za ta ba manufofin tsarin tattalin arzikin Nijeriya mutunci da kima. Har wala yau kuma ya ce wannan ziyarar ya kawo ta ne bisa ga  umurnin fadar shugaban kasa da ya bashi don samun tabbacin ci gaban da aka samu a matakin kulle kan iyakokin da aka dauka a yan kwanakin nan. Hamid Ali ya gargadi gamayyar jami’an kula da shige da fice a kan iyakokin Nijeriya da cewa su tabbatar wajen kulle kan iyakokin baki daya tare da taka birki ga duk wani wanda ke kokarin yi wa wannan umurni na Nijeriya karan-tsaye. “Saboda haka wadannan kan iyakokin Nijeriya za su ci gaba da kasancewa a kulle har sai kasashen da suka hada makwabtaka da Nijeriya sun yarda a hukumance da tsaretsare da manufofin tattalin arzikin mu sannan mu bude su”. “Wannan shi ne karon farko a tarihin Nijeriya wanda muka kafa gamayyar rundunar tsaron kan iyakoki wadda ta kunshi sojoji da jami’an shige da fice, magireshin da yan-sanda. Kuma gwamnatin tarayya ta dauki matakin ne don samun tabbacin cewa an rufe kan iyakokin baki daya”. In ji shi.

Exit mobile version