Rahotanni sun bayyana cewa kan wasu daga cikin yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ya rabu biyu sakamakon ƙarin albashin da akayiwa ɗan wasan ƙungiyar, Marco Asensio bayan ya sake sabon kwantaragi.
Acikin satin da ya gabata ne dai ɗan wasan ya sake sabon kwantaragi da real Madrid sannan kuma aka kara masa albashi inda a yanzu yana daya daga cikin masu daukar albashi mai tsoka a ƙungiyar.
Yan wasa irinsu Toni Kroose da Casemiro an bayyana cewa basuji dadin abin ba inda suma suka buƙaci ƙarin albashin tun farko amma ƙungiyar bata ƙaramusu ba duk da cewa suna ganin sun cancanta a ƙara musu albashin.
Asensio dai ya bi sawun yan wasa irinsu Isco da Carɓahal da benzema da marcelo wajen sake sabuwar yarjejeniya da ƙungiyar.