Sakamakon zaben kananan Hukumomin Jihar Kano ya nuna yadda al’ummar Karamar Hukumar Tarauni suka nunawa Alhaji Ababakar Zakari cewa su halattatun ‘yan amana ne, jawabin haka ya fito daga bakin zababben Shugaban Karamar Hukumar ta Tarauni Hon. Ababakar Zakari Jim kadan da kada kuri’arsa a mazabar sa dake Unguwar Gano.
Sabon shugaban Karamar Hukumar ta Tarauni ya nuna gamsuwarsa bisa yadda aka gudanar da sahihin zabe wanda kowa ya aminta da yadda aka tsara zaben. Babu shakka dole ajinjinawa Hukumar zaben mai zaman kanta ta Jihar Kano bisa kyakkyawan tsare tsare wanda hakan yasa aka samu nasarar da ake fata. Yace banyi mamaki ba musamman kasancewar na rike kujerar wakilin al’ummar karamar Hukumar Tarauni a majalisar dokokin Jihar Kano, wanda Alhamdulillah mun bada gagarumar gudunmawa.
Da aka tambaye shi ko ya yake kallon kauracewa zaben da PDP tsagin Kwankwasiyya suka Yi, sai amsa da cewa, Wanda Bai San Gari ba sai ya saurari daka, jama’ar Kano sun dawo daga rakiyar ‘yan gangan, Kuma tuni akayi jana’izar PDP a Kano, Don tabarmar kunya ce, shi jagoran nasu yasan Kaye zai Sha, hakan yasa suka daure ‘yan jama’ar tasu da igiyar Zato.
Daga nan sai Ababakar Zakari ya mika sakon godiyarsa ga dubun dubatar jama’ar da suka Yi fitar dango suka zabi ‘yan takarkarun Jam’iyyar APC bakidaya.