Kwamishinan Kananan hukumomi da masarautun gargajiya na Jihar Nasarawa, Alhaji Haruna Iliya Osegba ya bayyana haka a taron hadin gwiwa na biyan albashin Kananan hukumomi a makon da ya gabata.
Kwamishinan ya ce, abin da kananan hukumomi suka samu daga asusun Gwamanatin Tarayya kenan na albashin watan uku.
Ya kara da cewa, Kananan hukumomi 13 da suke jihar tare da yankunan raya kasa da ke fadin jihar sune za su rarraba wannan albashin.
Ya ce, wannan kudaden sun zo ne cikin asusun hadin gwiwa da jihar ke yi da Kananan hukumomi.
LEADERSHIP A Yau ta ziyarci wannan zaman da ya hada Shugabannin Kananan hukumomi 13 tare da Shugabannin kungiyar kwadago na jihar Nasarawa da Kungiyar Ma’aikatan Kananan hukumomi.
Kwamishinan ya ce, wannana kudaden za a biya albashi ne ga ma’aikatan Kananan hukumomi tare da Sarakunan gargajiya.
Ya ce, “A wannan watan muna saran Ma’aikatan za su samu albashi dai dai da yawan Ma’aikatan kowacce Karamar hukuma.”
Ya kara da cewa wasu kananan hukumomi za su samu kashi 65% sannan wasu za su samu kashi 85% ya ce, ya danganta da yawan ma’aikatan da karamar hukuma ke da su saboda wata karamar hukumar tana da ma’aikata da ya wa, wasu kuma nasu bai kai wancan yawa ba. Shi ya sanya albashinsu ba zai zama iri daya ba.
Ya ce, muna fatan nan gaba harajinmu ya karu, kuma tattalin arzikin kasa ya gyaru ta yadda za a rika biyan kowanne ma’aikaci albashi 100 bisa 100.
Kwamishinan ya yi kira ga ma’aikatan dasu rika daure wa suna zuwa bakin aiki akan lokaci saboda Gwamnatin Jihar Nasarawa karkashin jagorancin Gwamna Umar Tanko Al-makura kullum burinta ta biya ma’aikaci hakkinshi, shi ya sa da zarar albashi ya shigo gwamnati ke kokarin biyan ma’aikata abin da ya samu saboda su ma su ji dadi an bi ya su hakkinsu a kan lokaci.