Connect with us

HATSIN BARA

Kanawa A Komar Lugga

Published

on

Kano daya ce daga cikin manyan masarautun kasar Hausa wato mazaunin Hausawa a yau.
Kano Masarauta ce mai kwarjini a cikin kasashen Hausa da kewaye. Kano na daya daga cikin biranen da Turawan mulkin mallaka suka yaka har suka kwace ikon gudanarwarta, suka dora
ta bisa mulkin son rai irin nasu.
Tilas mu karfafa cewar “Mulkin son rai irin nasu.” La’akari da furucin babban jagoran dakarun tabbatar da mulkin mallaka a kasar Hausa wato Baturen nan da ake kira Gwamna Lugga, bayan da aka fafata yaki tsakanin Kanawa da dakarunsa, karkashin jagorancin Kanar Morland Maimadubi a shekarar 1903 a cikin birnin Kano, lokacin da Turawan suka samu nasarar kashe Waziri Amadu, (wazirin Sarkin Kano Aliyu), sai suka shiga shirye-shiryen nada Wambai Abbas a matsayin sarkin Kano na riko. A yayin wannan nadin nashi ne Gwamna Luggan ya sanar da shi cewa, “Turawa ba za su shiga harkar addininsu ko al’adarsu ko dokokinsu ba, muddin dai ba su kauce wa tsarin Turawa ba.”
“…Muddin dai ba su kauce wa tsarin Turawa ba.” Wannan gaba ce mai muhimmanci abar lura, wadda da ga ita za mu iya fahimtar cewa, Turawan sun zo da wani bakon al’amari ne, wanda kuma suke da yakini kan cewa zai iya sabawa da ra’ayin mutanen da suka zo suka tarar, wato Hausawa. Amma ko bayan waccan magana da Gwamnan ya sanarwa da Wambai Abbas a yayin nada shi a matsayin Sarkin Kano na riko, Gwamna Lugga ya kara sanar masa da cewa, “Yanzu tun da Turawa ke mulkin kasar nan, kuma su ne za su zabi wanda zai zama sarki da kuma wanda zai yi kowace irin sarauta, amma za a bar mutane su yi abin su kamar yadda suka gada. Zartar da al’amura duka yana wurin Gwamna kuma Gwamna yana iya tube sarki saboda rashin iya mulki.
Haka kuma a game da addinin Musulunci, Turawa ba za su hana ci gaba da yadda ake yi ba. Dukkan gidajen shari’a da majalisun sarakuna za a tabbatar da ikonsu bisa ga yadda Razdan ya ga ya kyautu. Kuma ba za a yarda a kashe kwabo ba sai da sanin Razdan. Za a hana toshiya da cin hanci da mummunan zalunci duka. Wadansu irin laifuffukan kuwa za a hukunta su a dakin shari’a na lardi, wato shari’ar da ta shafi mutanen da su ba ‘yan kasar nan ne ba, ko ma’aikatan gwamnati duk a can za a kai su a yi musu shari’a. Gwamnati kuma za ta aza kudin haraji iri-iri bisa ga yadda Gwamna ya ga ya dace, sai dai harajin da za a saka, ba za a bar zalunci ya shiga cikinsa ba. Masu fatauci da ‘yan kasuwa duk za a taimake su yadda za su ci gaba da sha’anoninsu, arzikinsu ya karu. Sarki ba zai saka musu harajin kome ba, sai irin abin da Gwamna ya ce ga yadda za a aza musu. Za a bar kowa ya yi amfani da wurin da yake rike da shi, in gona ce ko gida, sai fa in gwamnati ta ga tana da bukatar wurin don yin wani aiki wanda zai amfani kasar baki daya.” (Galadiman Daji 2008:24)
Shin Turawan sun cika wannan alkawarin da suka dauka ko ba su cika ba? Sannan kuma ma, ko me ya sa Gwamnan ya yi wannan bayanin? Shin Ko a kasar Hausa kafin zuwan su Turawan babu ingantaccen tsarin mulki ne wanda Hausawan suke gudanarwa a tsawon rayuwarsu? A’a sam ba haka lamarin yake ba. Domin kuwa tun kafin zuwan Turawa kasar Hausa, da ma can Hausawa mutane ne masu tsarin shugabanci irin nasu a kusan dukkan al’amuran rayuwarsu na yau da kullum. Wadanda ma daga su din ne Turawan suka kwaikwaya, suka gina sabon tsarin mulkin mallakar da suka kafa a kasar ta Hausa.
Tun kafin zuwan Turawa kasar Hausa an shimfida mulki bisa tafarkin shari’a a karkashin daular Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo. Ana cikin wannan hali, sai Turawa suka fara shigowa kasar Hausa don yin binciken kasa da leken asiri. Umar (2008). To amma fa ko kafin Jihadin Shehu Usmanu Danfodiyo ma Hausawa suna da tsarin mulki irin nasu na tun asali.
Daga cikin ire-iren shugabancin Hausawa akwai Mai-unguwa. Gidajen gandu-gandu su ke haduwa su yi unguwa kuma akan zabi shugaba guda, wato “Mai-unguwa” ya dauki shugabancin sauran “Iyayen-Gandu” da iyalansu. A tsarin mulki, dukkan ayyukan da hukuma ke so ta yi a wannan unguwa, akan biyo ta wajen mai-unguwa, saboda shi ne ya san kowa da kowa a unguwar. Mai-unguwa a matsayinsa na shugaba shi ke yin sulhu da shirya jama’a idan wata rigima ta taso, musamman kamar rigimar gona, ko ta aure, ko fada, ko sata da dai makamantan wadannan.
Bayan Mai-unguwa kuma akwai Dagaci. A kauye inda unguwanni da dama suka hadu da kuma gidaje da yawa, a kan zabi shugaban jama’ar kauyen, wanda hukuma ce ke zabarsa, wannan shi ne Dakaci. A tsarin mulkin Hausawa Sarki ne yake nada Dagaci. Wannan dagacin shi ne zai dauki nauyin al’ummar garin, shi ne ke wakiltar Sarki da Hakimi a kauyensa, kuma shi ne mai kula da duk abin da hukuma za ta yi a kauyen. Ta kansa ne talakawa ke gabatar da bukatunsu ga hukuma. Dagaci yana daukar babban nauyi tare da taimakon masu unguwanninsa. Duk wata husuma da ta tashi tsakanin mutanen kauyen wacce ta shafi rayuwa ta yau da kullum, Dagaci ne zai yi kokari ya kashe wannan wutar ya sulhunta yadda za a
samu zaman limana da jin dadi. Duk jama’ar kauyen har da masu unguwanni suna karkashin shugabancin Dagacin suna kuma girmama shi sosai. A kullum, Dagaci a matsayin sa na shugaba, yana kokari ya ga ya kyautata wa jama’a ya kuma kawo ci gaba a kauyen.
Bayan Dagaci kuma akwai Hakimi, wanda a tsarin mulkin Hausawa, shi ne shugaban gari ko kasa wanda kauyukan dagatai suke karkashinsa. Shi ne wanda sarki yake nadawa dan ya shugabanci jama’ar garinsa. Hakimi shi ne ya ke kula da kauyukan da ke cikin yankin kasarsa. Duk abin da hukuma ta ke bukatar jama’a ta yi, sai ta aiko ta wajen Hakimi, shi kuma ya tara Dakatai da Masu-unguwanni ya ba su umarni. Hakimi a matsayinsa na shuga shi ne mai kwantar da duk wata rigima ko tarzoma da ta tashi a kasarsa. Shi ne mai yin shari’a ya sasanta jama’a a kan wasu matsaloli. Hakimi shi ne wakilin hukuma, kuma duk abin da hukuma za ta yi a kasarsa, sai an biyo ta wajen sa, ya yi jagoranci wajen yin abin. Duk jama’ar kasa suna ba wa Hikimi girma kuma suna daukar umarninsa. Hakimi a kullum bisa shugabancinsa, yana yin kokari ya ga cewa kasarsa da al’ummar kasar suna zaune lafiya da samun ci gaba da kuma isasshiyar lafiya.
Bayan kuma Hakimi akwai Sarki wanda shi ne babba a cikinsu. Shi ne shugaban al’umma a tsarin mulkin Hausawa. Duk Hakimai da Dagatai da Masu-unguwanni da sauran talakawa suna karkashinsa a matsayin mabiya.
Sarki shi ne mai daukar nauyin jama’a ta fannonin rayuwa ya kula da al’amuransu na yau da kullum ta fuskar zama. Sarki shi ne ke yi wa jama’arsa jagoranci a kan kowane abu da ya shafi rayuwa. Sarki shi ne baban kowa, dan haka ma ake ce da su “Iyayen jam’a.” A tsarin mulkin Hausawa, kome sarki ya ce ba a musa masa sai dai a yi kawai. Yana da cikakken mulkin mutanensa birni da kauye. Haka kuma idan muka dawo ta bangaren sana’o’in Hausawa zamu tarar da cewa, tun asali kowace sana’a a kasar Hausa tana da sarkinta, wato shugaban dukkan masu gudanar da irin wannan sana’ar, shi ne wakilinsu a wurin hukuma kuma duk abin da ya zartar bi ne nasu. Wannan tsarin ma shi Turawa suka kalla suka kwaikwaya wajen samar da shugaban ma’aikata, mai kula da al’amuran ma’aikata a tsarin mulki irin nasu.
Yanzu dai da wannan bayanin na sama mun fahimci cewa, Hausawa suna da tsarin mulki irin nasu tun kafin Jihadin Shehu Usmanu Danfodiyo balle kuma a yi batun zuwan Turawa. To idan haka ne, mene ne dalilin Turawan na tabbatar da tsarin mulkin mallaka a birnin mai dadaddan tarihi?
Shin ko mun san manufar zuwan Turawa Kano kuwa?

Abba Muhd Danhausa
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: