A ranar Asabar din da ta gabata, 16 ga Janairu, 2021, ne aka gudanar da zaben yankunan kananan hukumomi a dukkan fadin Jihar Kano. Wannan ya sa LEADERSHIP A YAU ta kewaya wasu mazabu, domin ganin yadda zaben ke gudana tare da jin ra’ayoyin mutane.
Babu shakka ra’ayoyi sun bambanta kan yadda muka ji daga bakin mutane daban-daban ta kowanne bangare. Akwai babbar mazabar Kaura-Goje, inda muka samu tattaunawa da wasu daga cikin wadanda suka halarci zaben.
Abdullahi Hadi Umar, daya ne daga cikin wadanda suka kada kuri’a a wannan filin makaranta, ya bayyana yadda zabe ke tafiya, inda ya ce ya yi nasa zaben kuma ya ga ana yin zabe lami-lafiya kalau sai dai rashin fitowar al’umma ne kawai, wanda wannan kuma yana nuni da cewa, a duba al’amuran matasa da kuma a tallafa musu, kuma a cewarsa, gaskiya wannan ya nuna cewa rashin aikin yi ya damu al’umma.
Shi kuwa Hon. Muhammad Sani Yau Nusa Kaura-Goje cewa ya yi, wannan zabe ana yin sa cikin kwanciyar hankali da nasara. Ya ce, tun da aka sa akwatin zaban nan daga safe zuwa yanzu babu wanda ya nuna wa wani ko dan yatsa, kuma ana ta kai-komo a cikin wannan fili babu wata matsala.
Shi kuwa Musa Muhammed Mabo cewa ya yi, zabe yana gudana kawai dai matsalar da aka samu ita ce rashin kawo kayan zabe da wuri, amma komai yana gudana kalau. Kuma cewa wannan zabe ba ‘yan adawa wannan ba gaskiya bane domin a wannan gurin akwai ‘yan jam’iyar PDP kuma suna wannan wajen kuma ga shi nan suna kare jam’iyarsu.
Shi kuwa Ta’ambo ya yi kira ga gwamnati da ta dinga taimakawa jama’a domin mutane suna cikin wani hali. “ Zuwanmu makarantar Dangana kuwa, nan ma mun hadu da Honarabul Ado Gambo Tsohon Kansila na mazabar Tudun Murtala, ya bayyana cewa an sami nasara domin daidai gwargwado an fito to wannan ma nasara ce.
A cikin wasu kuwa da ba su je wajen zaben ba, wani mai suna Labaran ya bayyana ra’ayinsa na kin zuwa wajen zaben, inda ya ce, ai ko ya je ko bai je ba tuni sun gama zabensu, don haka babu dalilin sa ya je ya sha wahalar banza.
Wata kuwa mai suna Halima ta ce ai ta yi amfani da wannan ranar wannan zaben, domin ta kwanta ta yi baccinta ya fi mata.