Haruna Akarada" />

Kanawa Za Su Cigaba Da Amfanar Ayyukan Gwamna Ganduje – Dan-Mutum

Tun bayar nasarar da Jam’iyyar APC tare da Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, suka samu a makon da ya gabata, har yanzu al’ummar Jihar Kanon na cigaba da fadin albarkacin bakinsu, inda a daidai wannan lokaci Alhaji Murtala dan Mutum kaura Goje, tsohon Shugaban Kasuwar Dawanau da ke cikin Birnin Kano, sannan dan gaba-gaba a gidan Sardaunan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya samu zarafin tattauna da wakilinnmu na LEADERSHIP A Yau, HARUNA AKARADA, akan wasu muhimman abubuwa da ya yi wa gwamnatin da ta samu wannan nasara tuni, musamman a bangaren da ya shafi Kasuwarsu ta Dawanau tare da gagarumar gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake Shugabantar wannan Kasuwa. Ga dai yadda tattaunwar tasu ta kasance:

Mai karatu zai so jin ko da wa muke tare?
Sunana Alhaji Murtala dan Mutum kaura Goje, tsohon Shugaban Kasuwar Dawanau da ke nan Kano.

A halin da ake ciki yanzu dai, tuni Kotu ta kori wancan kara da Jam’iyyar PDP ta shigar na kalubalantar nasarar da Gwamna Ganduje ya samu, amma kuma sai ga shi Jam’iyyar PDP ta sake daukaka kara, yaya kake kallon wannan dambarwa?
To, a nan gaskiya babu abinda za mu ce wa Allah, sai godiya bisa wannan baiwa da Ya yi mana, sannan Ya bayyana gaskiya a fili kowa ya gan ta akan wannan shari’a tamu. Kazalika, kowa ya san cewa, mai girma Dakta Abdullahi Umar Ganduje shi ne ya ci zabe, amma da yake ba ka taba rasa dan Adam da korafi, musamman akan irin wannan harka ta zabe sai suka kalubalanci wannan nasara da muka samu, suka kasa yin hakuri da abinda Allah Ya yiwa mutanen Jihar Kano, suka garzaya Kotu. Saboda haka ga dai irinta nan, domin kuwa zuwan nasu Kotu babu abinda ya harfar musu illa bata lokaci tare da tashin hankali na babu gaira babu dalili.

A matsayinku na wadanda aka yi ta faman fafutuka da ku har aka kai ga samun wannan nasara, wace shawara kake da ita musamman wajen zabo wadanda za su dafa wa mai girma gwamna da kuma yadda za a cigaba da rike ‘yan jam’iyya?
To gaskiya dai abubuwan da na ke son yin tsokaci akansu suna da yawa, amma da farko dai ko bako ne ya shigo Kano, ya san cewa lallai an samu canji karkashin Dakta Abdillahi Umar Ganduje, musamman idan aka yi duba da irin muhimman ayyukan da yake yi a fadin wannan jiha. Kazalika, maganar rike ‘yan jam’iyya, to gaskiya kowa ya san mu mutanen mai girma tsohon gwamna ne wato Sardaunan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, kuma mun yi duk abin yi wajen kawo wannan gwamnati domin ganin dorewarta. A nan kiran d azan yi ga shi mai girma gwamna shi ne, ka da ya manta da irin wadanda suka taimaka masa domin kawo wannan gwamnati, an ce yaba kyauta tukwici, wannan yasa muka tashi muka tsaya tsayin daka domin ganin wannan gwamnati ta kai labari. Sannan babu abinda za mu ce sai godiya ga Allah wanda shi ne ya shige mana gaba.

Kana daya daga cikin Shugabannin da suka taba yin jagorancin wannan kasuwa ta Dawanau, sannan ga dukkanin alamu akwai wasu ayyukan raya kasa da wannan kasuwa taku ke bukata, wane irin jan hankali za ka yi ga wannan gwamnati domin ganin kun amfana da ire-iren wadannan ayyuka?
Ko shakka babu, ba mu da abinda za mu cewa wannan gwamnati sai sam barka, domin da ma akan wannan kasuwar mun dade muna ta kiraye-kiraye, muna kuma da tabbacin wannan kasuwa za ta amfana da ayyuka iri daban-daban. Idan ka duba akwai titin da ya hade tun daga ‘Yan awaki ya kai har zuwa titin danbatta, wajen kilo mita biyar, kuma yanzu haka an kusa kammala shi, to ka ga ‘yan kasuwar Dawanau babu abinda za su cewa Dakta Abdillahi Umar ganduje, sai dai godiya, sannan su cigaba da yi masa fatan alhairi. Ina daya daga cikin mutanen da aka zagaya da mu a farkon shugabancina, muka bi wasu titina da za a zo za a yi mana su har da fitulu da za a sa a wasu kan titi nan cikin kasuwar, kuma fara wannan titi babu abinda za mu ce da Allah sai godiya, tun daga aiki nan mun ga an fara yi mana shi a cikin kasuwar.

Kasuwar Dawanau ta yi fice wajen sama wa Matasa ayyukan yi, wane irin kira za ka yi ga gwamnati wajen ganin ta baiwa wannan kasuwa kulawa ta musamman domin cigaba da kokarin rage zaman banza a tsakanin wadannan Matasa?
Babu shakka maganarka haka take, domin kuwa a duk fadin Jihar Kano Kasuwar Dawanau na daya daga cikin kasuwar da ke baiwa Matasa dama, musamman wadanda ba su da ayyukan yi, dai-dai gwargwado gwamnati na ba mu hadin kai ta fuskar a kawo ayyuka, sannan ga ayyukan nan ya fara shigowa cikin kasuwa, da a ce ana yi sau uku; to za mu ce muna yin maraba da hakan.

Sakamakon umarni da Gwamnatin Tarayya ta bayar na rufe iyakokin kasar nan, wace matsala a halin yanzu kuke fuskanta akan abinda ya shafi ire-iren kayan da kuke fita da su kasashen ketare?
Alhamdulillahi, domin kuwa a gaskiya mu dai har yanzu ba mu da wata matsala akan abinda ya shafi cigaban harkokinmu, kuma ba mu taba samun wata matsala ba. Hakan nan, ya kyautu al’ummar wannan kasa su fahimci cewa, shi fa gyara haka yake wani a yi shi daidai, wani kuma samu akasin haka. Sannan ni a nawa ganin, wadannan matakai da ake dauka za su kawo mana cigaba nan gaba kadan da yardarm Allah, amma fa sai an yi hakuri, babban fatanmu a nan shi ne wadannan iyakoki da aka rufe, nan ba da jimawa ba a sake bude su domin cigaba da harkoki na yau da kullum.

Exit mobile version