Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home LABARAI

Kangin Talauci: Dabarun Buhari Na Ceto Mutum Miliyan 100

by Sulaiman Ibrahim
March 22, 2021
in LABARAI
8 min read
Kangin Talauci: Dabarun Buhari Na Ceto Mutum Miliyan 100
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Nasir Gwangwazo, Abuja

  • An Taskace ‘Yan Nijeriya Miliyan 30 A Rajistar Al’umma Ta kasa
  • Yadda Ma’aikatar Jinkai Ta Tallafa Wa Marasa Galihu Lokacin kuncin Korona
  • Shin Ya Aka Yi Rabon Tallafin Abinci Lokacin Annobar Korona

Gwamnatin Tarayya ta ce ta rubuta sunayen mutane da ba za su gaza miliyan 30 ba a Rajistar Al’umma ta kasa (National Social Rajista, NSR) wadda za a yi amfani da ita a samu saukin ceto mutane miliyan 100 daga fatara a cikin shekaru 10 masu zuwa.
Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouk, ita ce ta  bayyana haka a taron Sakatarorin Dindindin na jihohi kan shirin gwamnati na magance matsalolin yau da kullum (National Social Safety Nets Project, NASSP), wanda aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja.
Ministar ta samu wakilcin Sakataren Dindindin a ma’aikatar, Alhaji Bashir Alkali, a taron.
Ta ce aikin da aka dora wa ma’aikatar na gudanar da shirin na NASSP tare da tallafin Bankin Duniya, ana yin shi ne domin a rage fatara da matsalolin yau da kullum a Nijeriya.
Hajiya Sadiya ta ce an tsara shirin na NASSP ne domin ya kasance ya na da ofisoshi daga matakan tarayya zuwa jihohi, har zuwa yankunan kananan hukumomi, wato ya nuna matakai uku na gwamnati.
Ta ce, “A yanzu, rajistar NSR ta na da sunayen ‘yan Nijeriya miliyan 30 daga jihohi 36 da Yankin Babban Birnin Tarayya daga gidajen matalauta guda miliyan bakwai. Idan an kara lissafawa, za a ga cewa an samo wadannan gidajen ne ya zuwa yanzu a yankunan kananan hukumomi 699, mazabu 8,161 da al’ummomi 81,776 a sassan kasar nan.
“An samar da rajistar ta NSR ne ta hanyar yin amfani da tsarin fasalin kasa da al’umma, ta hanyar amfani da jama’ar unguwa, wanda ofishin kula da tsarin a jiha (SOCU) ya ke tattarawa a kowace jiha.
“Ofishin raba kudi na kasa (National Cash Transfer Office, NCTO), a yanzu ya samu gidajen matalauta da ke amfana da shirin guda 1,632,535 a al’ummomi 45,744 daga unguwanni 5,483 na yankunan kananan hukumomi 557 da ke jihohi 35 da yankin Abuja.”
A cewar Sadiya, wannan na nuna cewa an samu mutum 8,100,682 a gidajen da ke cin moriyar shirin ta hanyar wakilin kowane gida wanda ake kira ‘Caregiber’ ko ‘Alternate Caregiber’ wanda ake biya sau biyu a wata (N10,000).
Ta kara da cewa a yanzu, gidaje 991,965 ne su ke karbar kudi a jihohi 28 da yankin Abuja. Ta nanata cewa dukkan wadannan abubuwa an yi su ne da nufin cika burin Shugaba Muhammadu Buhari na ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga matsananciyar fatara.
Ta ce, “Don haka, akwai bukatar a daidaita ofisoshin shirin na SOCU da yadda ake gudanar da shi. Hakan na da matukar muhimmanci.”
A nasa jawabin, Babban Kodineta na NASSCO, Mista Apera Iorwa, ya ce manyan sakatorin shirin a jihohi su ne ma’aikata masu sanya ido kan shirin a jihohin su.
Ya ce, “Akwai bukata a gare mu da mu rika haduwa a kai a kai domin mu yi nazarin al’amura da tsare-tsare tare da gano hanyar da za a samu cigaban shirin.”
Mista Iorwa ya ce tilas ne manyan sakatorin su tashi tsaye domin su tabbatar ba a kautar da manufar shirin a jihohin su ba.
Ya ce an tsara cewa jihohi za su mayar da kudin ga Bankin Duniya domin za a yi binciken kowane asusu kuma idan aka gano cewa kudi sun salwanta, to tilas ne a dawo da su a biya.
Haka shi ma Kodinetan Shirin Tiransifar Tsabar Kudi na kasa (Conditional Cash Transfer), Ibrahim Jafar, ya ce tafiya tare da dukkan masu ruwa da tsaki  a shirin ya na da muhimmanci ga samun nasarar shirin.
Ya ce akwai matukar muhimmanci a san bambancin da ke akwai tsakanin Rajistar Masu Cin Moriya ta kasa (National Beneficiary Register) da Rajistar Al’umma ta kasa (National Social Register).
Ya bayyana cewa akwai wasu matsaloli da ake samu wajen biyan kudi, to amma nan ba da dadewa ba za a warware yawancin su.
Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) ta ruwaito cewa a yayin da wasu Sakatarorin Dindindin su ke gode wa Ma’aikatar Harkokin Jinkai saboda wannan damar da aka samu, wasu kuwa sun koka kan babbar tazarar da aka samu tsakanin su da SOCU saboda NASSCO.
A lokacin da ya ke magana kan hakan, Mista Iorwa ya nanata cewa daga yanzu za a fara magance matsalar, kuma duk wani bayani da aka mika wa SOCU to za a mika shi ga su Sakatarorin Dindindin din.
Baya ga Hukumar NCDC wadda Gwamnatin Tarayya ta dora wa alhakin dakile cutar korona da hana ta bazuwa a cikin kasa, babu wata hukuma a kasar nan da ta yi tasiri a cikin al’umma kamar Ma’aikatar Ayyukan Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwar Marasa Galihu.
Irin yadda wannan ma’aikata ta zabura a cikin kankanin lokacin ta rika bijiro da hanyoyin bayar da tallafin rage wa marasa galihu radadin kuncin rayuwa a lokacin kullen korona da bayan kullen, hakan ya kara tabbatar da cewa Minista Hajiya Sadiya Umar Farouk da ke shugabancin wannan ma’aikata, ta taka muhimmiyar rawa wajen tsamo dimbin marasa galihu a kasar nan daga cikin halin kaka-ni-ka-yin da su ka fada, a lokacin da cutar korona ta tsayar da dukkan gudanar da al’amurra a kasar nan.
Minista Sadiya ta zama uwa mai bada mama ga marasa galihun da ta rika raba wa kayan tallafin korona a fadin  jihohi 36 da BABBAN BIRNIN TARAYYA Abuja, a cikin kankanin lokaci. Sai da ta kai a lokacin duk inda ka ji ana maganar cutar korona, to kuma sai ka ji ana maganar tallafin korona, tamkar ma tallafin korona din shi ne maganin ita cutar koronar.
Shirin raba tallafin abinci da kudi a lokacin korona, shi ne abin da ya fi daukar hankali. Ma’aikatar Harkokin Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwa ta kasance ma’aikatar da ta fi kowacce kusanci da talaka saboda ita ce ke fara sanin halin da talaka ke ciki, kuma ita ke yin tattaki har gida ta same shi ta share masa hawaye, ko kuma ta rage masa radadin kuncin talaucin da ke addabar shi.
Shekara daya bayan hawa mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, an fito da tsare-tsaren inganta rayuwar marasa galihu, wanda ake kira ‘Social Interbention Programmes’, wato SIPs a takaice.
Talakawa da sauran marasa galihu sun rika samun tallafi daban-daban daga irin wadannan tsare-tsaren da shirye-shirye. To kuma sai ire-iren wadannan tallafi su ka hada da ayyukan da Hukumar Kula da Masu Gudun Hijira da Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ke yi na kai agaji ga wadanda yaki ko rikici ya raba su da garuruwan su, wani ibtila’in gobara, ambaliya ko wata musiba ta afka wa.
Domin kara wa shirin tallafa wa marasa galihu karfi da karsashi, Shugaba Buhari ya hade wadannan hukumomi ko shirye-shirye kusan shida a wuri daya, y kirkiro sabuwar ma’aikata sukutum ya saka su a karkashin ta.
Hausawa sun ce wanda ya san hanya shi ne dan aike na kwarai. An tabbatar da haka a lokacin da Buhari ya nada Hajiya Sadiya Umar Farouk Ministar Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwa, wadda da ma irin ayyukan da hukumar ta ke yi kenan, kafin a nada ta minista, wato Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira.
Babu abu mai faranta rai ga talaka kamar ya ga gwamnati ta nuna kulawa da shi, ta yadda ta ke bin sa har cikin gida da kaya ko ayyukan tallafin rage radadin talauci daban-daban. A ba ka kayan abinci. A ba ka kudin cefane, kuma a ba ka lamunin kafa kan ka ta hanyar ranta maka jarin fara sana’a ko bunkasa sana’ar dogaro da kai.
A cikin shekara daya da kafa ma’aikatar, Minista Sadiya ta nuna lallai ita ce wadda ta fi sauran mukarraban wannan gwamnati kusanci da talaka, kuma da ma ayyukan nata dungurungum duk na kulawa da talakawa ne.
Ayyukan tallafin da marasa galihu ke amfana da su a karkashin Ma’aikatar Agaji su na da yawa. Akwai hanyoyi daban-daban, wadanda an san su, amma da yawa wasu ba su fahimci yadda ayyukan su ke ba. Wasu ayyukan kan je wa talaka ta hannun wasu hukumomi da ke karkashin kulawar ministar. Wasu kuma na zuwa ne kai-tsaye daga nata ofishin ko ma’aikatar.
Ko dai talaka ya amfana a karkashin Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ko a karkashin Shirin Muradun karni (SDGs) ko Shirin Inganta Rayuwar Marasa Galihu (NSIP), wanda ake tura wa marasa galihu kudin rage radadin talauci.

Tallafin Kayan Abinci:
Gwamnatin Tarayya na tanadar abinci mai tarin yawa ta adana a cikin manyan rumbunan ta. Ana kiran wannan tanadi ajiya maganin wata rana. Ranakun da ake magana su ne aukuwar ambaliya, gobara, fari (wato karancin ruwan sama ko wata annoba da ta yi sanadin haifar da karancin abinci). To duk sai gwamnati ta sa ana diba daga wadannan rumbunan ana rabawa a matsayin tallafi.
Akasarin abin da aka fi tanada sun hada da gero, dawa, masara, wake da wasu nau’ukan kayan abinci. Ana kuma raba wa talakawa shinkafa mai tarin yawa ita ma, mafi yawa daga wadda jami’an kwastan ke kamawa a hannun masu fasa-kwauri.

Shirin Tallafin Abinci Da Kudi A Lokacin Korona:
Wannan shiri shi ne ya fi kowace daukar hankalin jama’a, saboda an kirkiro shi a wani lokaci guda, kuma mafi yawa jama’ar kasar nan ana zaman dirshan a gida.
Shirin ya gamu da sa-idon jama’a saboda da yawa sun yi masa karkatacciyar fahimta, duk kuwa da cewa Shugaban Kasa ya yi bayani dalla-dalla cewa ga rukuni da bangare da kuma jihohin da za su amfana da tallafin abincin da kuma kudaden.
Buhari, a cikin jawabin sa na biyu, a kan halin kuncin da ‘yan Nijeriya su ka shiga sanadiyyar barkewar korona, ya sanar cewa Gwamnatin Tarayya za ta raba kayan abinci har metrik tan 70,000.
Wannan tulin abinci kuwa, ba a ce gaba dayan kasar nan za a raba shi ba. Buhari cewa ya yi za a raba kayan abincin a wasu jihohi 13 da kuncin zaman gida tilas saboda korona ya fi shafa. A wadannan jihohi ma, cewa aka yi mafi yawan tallafin kayan abincin a karkara za a raba.

Ya Aka Yi Rabon Tallafin Abinci A Lokacin Korona?

Minista Sadiya ta kaddamar da rabon abinci da kudade lokacin korona a jihohi biyu (Legas da Ogun) da kuma Gundumar Babban Birnin Tarayya. Wadannan jihohi biyu da Abuja, an raba masu tirela 276 makare da kayan abinci.
Sauran jihohi kuwa duk ma’aikatar ta damka kayan abincin ne ga gwamnonin jihar. Wannan ya sa da yawan mutane ke ganin cewa kamar Gwamnatin Tarayya ba ta raba a jihar su ba, duk kuwa da cewa su na cikin lissafi.

Tallafin Rage Radadin Korona:
Wannan tallafi dai ya fi maida hankali ne wajen kai tallafi ga bangarorin al’umma marasa galihu, kamar sansanonin masu gudun hijira, nakasassu da musakai, matalauta da fakirai, masu kananan sanano’in da jarin su ba zai iya ciyar da su ba, da kuma sauran jama’a masu rauni saboda kuncin rayuwa.
A baya yawaci an lissafa kayan da wannan ma’aikata ta rika rabawa da su ka hada da masara, shinkafa, gero, dawa, sukari, man girki da tumatir da kuma taliya, wadanda aka raba a jihohi 36 da Babban Birnin Tarayaya Abuja.
An rika raba wa matan karkara daga masu shekaru 18 zuwa 50 naira 20,000 kowace. A karkashin wannan shiri an ware mata 120,000 a cikin kananan hukumomi 774 na jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Sannan kuma an rika raba wa marasa galihu tallafin kudade a karkashin shirin CCT, inda aka rika tura masu naira 20,000, matsayin kudaden alawus din watanni hudu a lokaci guda.
An rika bai wa mata da maza kananan ‘yan tireda tallafin kudade da lumuni a karkashin Trader Moni da Market Moni. Dubbai sun ci moriyar wannan shiri a lokacin korona.
An rage wa iyayen yara da su kan su yaran radadin kuncin korona a karkashin Shirin Ciyar da ‘Yan Makaranta daga Gida.
A karkashin wannan shiri, an rika bayar da kayan abinci ne dimbin gidajen da su ka ci moriyar. An rika ba su shinkafa, wake, man girki, man ja, tumatir, kwai da gishiri.
A jihohin Kano da Legas da Gundumar Yankin Abuja kuwa, an raba wa marasa galihu kudi da kayan abinci a karkashin Shirin Tallafin Gwamnatin Tarayya da Majalisar Dinkin Duniya.
An kashe dala milyan hudu a karkashin wannan shiri, inda Gwamnatin Tarayya ta rika raba kayan abinci, ita kuma Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da tallafin kudade.
Wannan shiri kuwa ya yi tasiri sosai a cikin al’umma wadanda kuncin rayuwa ya yi wa katutu, sakamakon tsaida harkokin komai a lokacin kullen Korona.
A takaice wannan ma’aikata ta yi rawar gani sosai wajen ceto marasa karfi a wannan mawuyacin hali da aka shiga. Kuma har yanzu ta na ci gaba da gudanar da ayyukan ta na agaji da jinkai, a matsayin  ma’aikatar na gatan marasa galihu a cikin al’umma.

SendShareTweetShare
Previous Post

Ba-ta-kashin Binuwe: Gwamna Ortom Na Farfaganda Don Bai Son Biyan Albashi – Fulani

Next Post

Iyaye Da Abokan Karatun Daliban Da Aka Sace Sun Rufe Hanyar Zuwa Filin Jirgin Sama Na Kaduna

RelatedPosts

Mafi Yawan Kamfanonin Ma’adanai Ba Sa Bin Ka’idar Aiki A Nijeriya – Adamu Nasko

Mafi Yawan Kamfanonin Ma’adanai Ba Sa Bin Ka’idar Aiki A Nijeriya – Adamu Nasko

by Sulaiman Ibrahim
38 mins ago
0

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna An yi kira ga gwamnatin...

Kwazon NIS A Fagen Kula Da Shige Da Ficen Kasa Da Tsaron Iyaka

Kwazon NIS A Fagen Kula Da Shige Da Ficen Kasa Da Tsaron Iyaka

by Sulaiman Ibrahim
44 mins ago
0

A wata ganawar da ya yi da kafofin watsa labarai,...

‘Yan Ta’adda Sun Kona Ofishin ‘Yan Sanda A Inugu

‘Yan Ta’adda Sun Kona Ofishin ‘Yan Sanda A Inugu

by Sulaiman Ibrahim
20 hours ago
0

Daga Sulaiman Ibrahim Hankula sun kara tashi a wasu yankuna...

Next Post
Iyaye Da Abokan Karatun Daliban Da Aka Sace Sun Rufe Hanyar Zuwa Filin Jirgin Sama Na Kaduna

Iyaye Da Abokan Karatun Daliban Da Aka Sace Sun Rufe Hanyar Zuwa Filin Jirgin Sama Na Kaduna

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version