Daga Bello Hamza, Abuja
Shugaban hukumar kula da harkar yawon bude ido ta kasa, ‘National Institute for Hospitality and Tourism (NIHOTOUR)” Alhaji Nura Kangiwa ya yi alkawarin tallafa wa masu otal-otal da wuraren bude ido don karfafa ma’aikatansu da makaman sanin aiki ta yadda za su gabatar da harkokin su yadda ya kamata.
Kangiwa ya yi wannan alkawarin ne a yayin da ‘yan kungiyar masu otal na yankin Abuja karkashin jagorancin shugabar kungiyar, Mrs Funmi Kazeem suka kai masa ziyara a Abuja.
”Manyan manyan otal ba shi ne ke nuna karfi da kyawun abubuwan da suke gudanarwa ba, amma yadda suke daukar abokan huldarsu da mahimanaci shi ne abin lura,” inji shi.
Ya ce, za a iya samar da ayyuka ga abokan hulda ne kawai in har an horas da ma’aikata sun kuma san mutumcin abokan huldarsu, ta haka ne za su samu bayar da ayyuka ga abokan huldar su yadda ya kamata.
Ya kuma bukaci ‘yan kungiyar masu otal din (HOFA) da su tsayu wajen kula da muhallinsu don ta haka ne masu hulda da su za su yi sha’awar sake dawowa don morar abin da otal din ke bayarwa.
Ya kuma taya sabbin shugabanin kungiyar murnar lashe zabe ya kuma shawarce su da su tafi tare da dukkan ‘yan kungiyar don samun nasarar da ya kamata.
A jawabinta tuun da farko, shugabar kungiyar, Mrs Kazeem, ta bukaci karin hadin kai daga gwamnati ta kuma yi alkawarin bayar da goyon baya don cimma dukkan tsare-taren gwamnati na bunkasa bangaren otal-otal na kasar nan.