’Yan bindiga sun kara kai wani hari a hanyar Kaduna zuwa Zariya a , a jiya. Cikin matafiyan da suka tsare har da dan uwan wani tsohon dan majalisa mai wakiltar mazabar Igabi. Har sun ji masa miyagun raunuka, yanzu haka yana asibitin sojoji na 44 ana kulawa da lafiyarsa Wasu ‘yan bindiga ne da ba’a san ko su waye ba suka kai wa dan uwan wani tsohon dan majalisa farmaki a hanyarsa ta Kaduna zuwa Zariya, inda suka bude masa wuta.
‘Yan bindigar sun tsare ababen hawa a wuraren Kwanar Tsintsiya da ke Karamar Hukumar Igabi ta hanyar Kaduna zuwa Zariya. Cikin matafiyan har da dan uwan Alhaji Kabir Muhammad, dan uwan Hon. Muhammad Abubakar Mamadi, tsohon dan majalisa mai wakiltar mazabar Igabi.
Yanzu haka yana asibitin 44 na sojoji da ke Kaduna ana kulawa da lafiyarsa. Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarada da sanar jiya. Ya ce bataliyar rundunar sojin Nijeriya sun samu nasarar ritsa ‘yan ta’addan, inda suka kashe 1, sauran kuma suka tsere da raunuka sakamakon ragargazar da suka sha da alburusai.