Connect with us

LABARAI

Kano: An Cafke Wacce Ta Kwara Wa Mijinta Ruwan Zafi Kan Bashin Naira 60

Published

on

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta tabbatar da kama wata mata mai suna Zahira Shu’aibu bisa zargin kwarawa mijinta ruwan zafi a jikinsa har ya kone.

Mai Magana da yawun runndunar ‘Yan Sandan Jihar Kao DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an kama matar ne wanda ake zargi bayan faɗa ya kaure tsakaninsu wanda mijin ya daketa ita kuwa ta kwara masa ruwan zafi har ya ƙona cikinsa, cinyoyinsa da ƙafarsa Tuni aka garzaya da su babbar helkwatar ‘Yan Sanda da ke Bompai don ci ggaba da bincike.
Mijin mai suna Abdulmitallib Gambo ya bayyana cewar, ya bawa matar tasa umarni da ta yi mu su girki sai ta ce tana binsa bashin kuɗin cefane kuma bai biya ba, wannan ne sanadin da suka samu saɓani.
Matar mai suna Zahira ta amsa cewa tabbas ta watsa wa mijin nata ruwan zafi.
Advertisement

labarai