Kano Pillars Ta Sha Kashi Har Gida A Hannun Lobi Stars

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta sha kashi har gida a hannun kungiyar kwallon kafa ta Lobi Stars dake garin Makurdi da ci 1-0 a gasar Firimiyar Najeriya bayan da dan wasan Lobi Stars Douglas Achiv ya zira kwallon cikin minti na 62 da fafatawar.
Karo na biyu kenan da Kano Pillars take tashi ba tare da samun nasara ba bayan da ta yi canjaras daya sannan kuma an doke ta a guda daya kuma  yanzu haka dai kungiyar ta Pillars na mataki na 17 a teburi da maki daya kacal ita kuwa Lobi Stars tana mataki na biyar da maki shida.
Kano Pillars dai tana buga wasanninta a gida ne ba tare da ‘yan kallo ba bayan da a shekarar data gabata magoya bayan kungiyar sukayi laifi aka dakatar dasu daga shiga kallon wasan kungiyar sannan kuma aka dakatar da dan wasa Rabi’u Ali sakamakon laifin daya aikata tsawon wasanni tara.
Ita ma kungiyar kwallon kafa ta Enyimba International ta doke Akwa United ne daci 3-1 ya yinda kungiyar kwallon kafa ta MFM taje har gida ta doke Enugu Rangers sai kuma sababbin hawowa Jigawa United wadanda sukayi rashin nasara akan kungiyar Delta Force daci 4-1.

Sakamakon Wasannin Da Aka Buga:
Kano Pillars 0 – 1 Lobi Stars
Abia Warriors 1 – 1 Sunshine Stars
Delta Force FC 4 – 1 Jigawa Golden Stars
Enugu Rangers 0 – 1 MFM FC
Enyimba 3 – 1 Akwa United
Heartland Owerri 1 – 1 Akwa Starlets
Ifeanyi Ubah United 1 – 0 Rivers United FC
Katsina United 1 – 0 Nasarawa United
Plateau United 2 – 1 Wikki Tourist
Warri Wolves FC 2 – 0 Adamawa United

 

Exit mobile version